'Yan Bindiga Sun Kai Mugun Hari Arewa, Sun Kashe ’Yan Sanda da Mutanen Gari

'Yan Bindiga Sun Kai Mugun Hari Arewa, Sun Kashe ’Yan Sanda da Mutanen Gari

  • 'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari kauyuka daban-daban a Katsina inda suka kashe kimanin mutane 22
  • An ce 'yan bindigar sun kuma kashe jami'an 'yan sanda hudu da kuma 'yan kungiyar tsaro ta KSCWC guda biyu a wannan harin
  • A zantawar Legit Hausa da Baba Bala Katsina, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya nuna damuwa kan matsalar tsaron jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta ce ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 22 a kauyukan Gidan Bofa da Dan Nakwabo a karamar hukumar Kankara ta jihar.

An ce ‘yan bindigar sun kai hari a kauyukan biyu ne da yammacin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

Yan sandan sun yi magana kan harin Katsina
'Yan bindiga Sun kashe mutane 20 da 'yan sanda 4 a Katsina. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Maharan sun kashe mutane 15 a kauyen Gidan Boka da kuma wasu biyar a yankin Dan Nakwabo, inji rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq ya fitar a ranar Litinin, ya ce ‘yan bindigar sun kashe jami’an rundunar hudu; sufeto uku da kofur daya.

Har ila yau, ya ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu ‘yan kungiyar tsaro ta KSCWC guda biyu a wani harin kwanton bauna.

Harin 'yan bindiga: Abin da ya faru

Jaridar Vanguard ta ruwaito Abubakar Sadiq ya tariyo yadda 'yan bindigar suka kaddamar da hare haren yana mai cewa:

"Mun samu kiran gaggawa a ranar cewa 'yan bindiga sun kaddamar da hari a kauyen Gidan Baki da ke a Kankara, inda har sun kashe farar hula.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kara samun nasara, an harbe 'yan ta'adda a Kaduna

"Cikin gaggawa muka tura jami'anmu. A hanyarsu ta zuwa Gidan Baki ne suka gano cewa a kauyen Gidan Boka ne aka kai harin, a nan suka canja akalar tafiyarsu.
"Da isarsu kauyen Kurmeji ta hanyar Yar Goje, sai aka farmake su, suka fara fafatawa da 'yan bindigar. D.P.O na Kankara ya samu labari, ya jagoranci tawaga domin kai masu ɗauki."

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

Kakakin rundunar ya ce a yayin gudanar da bincike, an gano cewa 'yan bindigar sun kashe mutane 15 a kauyen Gidan Boka, sai wasu biyu da suka jikkata.

"Sun kuma yiwa motar mu ta sintiri kwantan bauna, inda suka kashe jami'ai hudu, da jami'an kungiyar tsaron Katsina (KSCWC) guda biyu, amma an kashe 'yan bindiga biyar."

Rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina ta ce tana kan gudanar da bincike, inda ta kara da cewa za a sanar da al'umma halin da ake ciki na gaba kadan.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

"Ina malaman Katsina suke?" - Baba Bala

Legit Hausa ta ji ta bakin Baba Bala Katsina, wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum na jihar kan matsalolin tsaro da kuma batun kisan mutane da 'yan bindiga suka yi.

Baba Bala ya fara ne da tambayar "Ina malaman jihar Katsina su ke?" wadanda ya ce su ne suka riƙa yi wa 'yan siyasa yakin neman zabe a 2023.

Mai fashin bakin ya ce yanzu da 'yan bindiga suka kashe manoma akalla 50 babu wanda ya fito ya yi magana a kai.

Haka zalika, Baba Bala Katsina ya yi kira ga dattawa da masu fada a ji a jihar da su kasance masu yin magana kan matsalar tsaro kamar yadda suka yi kan aikin tashar jirgi a baya.

"Yan bindiga sun kashe akalla manoma 50, amma babu wani mai fada a ji a Katsina da ya yi magana.
"A lokacin da za a dauke aikin gina filin jirgin sama daga Katsina ne kawai muka ji duriyarsu. Wannan ba dai dai ba ne."

Kara karanta wannan

Ana daf da gudanar da zabe, 'yan bindiga sun harbe jigon dan takarar PDP

'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kashe mutane 12 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.

Cikin waɗanda aka kashe har da yan sanda bakwai da mutum daya daga cikin kungiyar tsaro da gwamnatin jihar Zamfara ta samar a kwanakin baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.