"Yar Zamewa Kawai Ya yi," Fadar Shugaban Ƙasa ta yi Bayanin Faduwar Bola Tinubu

"Yar Zamewa Kawai Ya yi," Fadar Shugaban Ƙasa ta yi Bayanin Faduwar Bola Tinubu

  • Hadimin shugaban kasa kan kafafen sada zumunta, Olusegun Dada ya bayyana cewa zamewa da shugaban kasa ya yi ba wani babban lamari ba ne da zai cutar da shi
  • Ya bayyana haka ne a shafinsa na X biyo bayan faduwar shugaba Bola Ahmed Tinubu a filin Eagles Square yayin bikin ranar dimkuradiyya da ya gudana a yau Laraba
  • Dada ya ce zamewar zai iya samun kowa, har ya yi shaguben cewa gwara mutum ya fadi kuma ya tashi nan take da ya fadi amma ya gaza tashi bayan shekaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya magantu kan bidiyon faduwar shugaban kasa a yayin bikin ranar dimukuradiyya.

Kara karanta wannan

"Ina fatan lafiya": Atiku ya magantu bayan Tinubu ya zame har kasa a faifan bidiyo

Da alama ya fusata da yadda jama’a ke yada wa tare da maganganu kan zamewar shugaba Tinubu lokacin da ya ke kokarin hawa motarsa a filin taro na Eagle square da ke Abuja.

Tinubu
Fadar shugaban kasa ta ce faduwar shugaba Tinubu ba wani babban abu ba ne Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Martani a kan faduwar Bola Tinubu

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Olusegun Dada ya ce ɗan zamewa kawai shugaban ya yi, ba wani babban lamari ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shaidawa ‘yan Najeriya cewa shugaban ya na nan cikin koshin lafiya, domin tuni ma ya ci gaba da harkokin bikin ranar dimukuradiyya.

“Kowa zai iya zamewa” - Hadimin Tinubu

Yayin da kafafen sada zumunta ke ta yada yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zame lokacin da ya ke kokarin hawa motarsa yayin bikin ranar dimukuradiyya.

Hadimin shugaba Tinubu kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya bayyana cewa lamarin zai iya faruwa kan kowa, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya faɗi ƙasa yayin taron ranar dimokuraɗiyya, fadar shugaban ƙasa ta yi martani

Mista Olusegun a jerin sakonnin da ya yi ta wallafawa bayan faduwar, ya ce gwara mutum ya fadi ya tashi, da a ce ya fadi amma ya gaza tashi.

Da yawa daga masu amfani da kafafen sada zumunta na ta murna da faduwar, yayin da wasu ke ganin alama ce ta cewa gwamnatin Tinubu ta gaza.

Amma Dada Olusegun ya kare shugaban, inda ya ce dan tuntube ne kawai, kuma tuni ya koma bakin aiki.

Shugaban kasa Tinubu ya fadi yayin taro

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fadi kasa yayin da ya ke kokarin hawa motarsa a bikin ranar dimukuradiyya a yau.

Lamarin ya jawo maganganu tsakanin ‘yan Najeriya inda wasu su ka yin jaje, wasu kuma ke ganin alhakin ‘yan Najeriya ne ya kama shugaban kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.