Arthur Eze: EFCC Za Ta Ƙwato Kadarori 20, Motoci 10 da Wasu Ƴan Gida 1 Suka Sace
- Hukumar da ke yaki da masu yi wa dukiyar al'uma zagon kasa (EFCC) ta samu umarni daga kotun daukaka kara kan dukiyar Arthur Eze
- Kotun da ke Abuja ta umarci EFCC da ta karbe kadarorin da wasu 'yan gida daya, Olisaebuka Eze da Onyeka Eze suka sace wa Arthur Eze
- A shekarar 2022, EFCC ta fara samun umarnin kwace kadarori 20, motoci 10 da agogon hannu uku na attajirin dan kasuwar na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin karbe kadarorin da wasu ’yan uwa biyu, Olisaebuka Eze da Onyeka Eze suka mallake su ta hanyar zamba.
Wata sanarwa da Dele Oyewale, kakakin hukumar EFCC ya fitar a ranar Litinin, ta ba da cikakken bayani kan shari’ar kotun da ta kai ga kwace kadarorin.
Hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar al'umma zagon kasa ta wallafa bayanin shari'ar a shafinta na yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan gida 1 sun damfari Arthur Eze
A shekarar 2022, EFCC ta yi nasarar kwace kadarori 20, motoci 10, da agogon hannu uku na wani attajirin dan kasuwar Najeriya, Arthur Eze.
Dan kasuwan ya kai karar Olisaebuka ga hukumar ne a shekarar 2020, bisa zargin sata, almubazzaranci, da kuma karkatar da kudin kamfaninsa, Oranto Petroleum Ltd.
Arthur Eze ya tafi hukumar EFCC
Arthur ya yi zargin cewa ’yan’uwan biyu sun sace masa kudin da aka kiyasta sun kai biliyoyin Naira da miliyoyin daloli.
Bayan kammala bincike, EFCC ta kama Olisaebuka da Nnadozie tare da saka takunkumi ga asusun ajiyar su na banki, biyo bayan umarnin kotu.
Olisaebuka da Nnadozie sun yi karar EFCC
A bisa rashin gamsuwa da umarnin karamar kotun na kwace kadarorinsu, Olisaebuka da Nnadozie suka shigar da kara daban-daban na neman soke umarnin a wata babbar kotu.
Sai dai a hukuncin da ta yanke a ranar 7 ga watan Yuni, babbar kotun ta yi watsi da karar da ’yan’uwan suka shigar kuma ta tabbatar da kwace kadarorin tare da mika su ga dan kasuwar.
Su Olisaebuka sun garzaya kotun Abuja
Har ila yau, 'yan gida dayan sun ki karbar hukuncin da babbar kotun ta yi, inda suka garzaya wata babbar kotun Abuja da ke Apo, bisa zargin EFCC ta tauye musu hakkinsu.
Alkalin kotun, S.B. Begore, ya yanke hukuncin da ya yi masu dadi, inda ya nemi EFCC ta biya 'yan gida dayan diyyar Naira miliyan 10.
Kotun daukaka kara ta yi hukunci
Ita ma hukumar ta kalubalanci hukuncin kotun, kuma kotun daukaka kara ta soke hukuncin da alkali S.B. Begore na kotun Abuja ya yanke.
Kotun daukaka karar ta ba wadanda ake kara umarnin biyan diyyar N500,000 ga hukumar EFCC.
Zargin kisa: Kotu ta wanke Ado Doguwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke dan majalisar Doguwa/Tudun Wada a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga zargin kisan kai.
Baya ga wanke Ado Doguwa, kotun ta kuma umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya dan majalisar wakilan diyyar Naira miliyan 25.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng