Bidiyoyin Biloniyan Najeriya Yana Rabawa Matasa $100 Kowannensu Ana Tsak da Karancin Kudi

Bidiyoyin Biloniyan Najeriya Yana Rabawa Matasa $100 Kowannensu Ana Tsak da Karancin Kudi

  • An ga wani biloniya 'dan Najeriya, Arthur Eze Oparada a bidiyo yana raba kyautar $100 ga kowanne matashi a jihar Anambra
  • Bidiyon da aka wallafa a soshiyal midiya ya janyo cece-kuce, inda mutane da dama suke ganin kamar siyasa ce
  • Wasu kuma sun ce biloniyan ya yi fice da hidima ga al'umma, wanda hakan ya sa jama'a ke kaunarsa

Wani bidiyo da ke tashe na nuna yadda wani biloniyan 'dan Najeriya Arthur Eze yake rarraba $100 ga duk wani matashi a anguwarsa. Har yanzu ba a gano dalilin yin hakan ba, sai dai Arthur Eze ya yi fice wajan hidimta wa al'umma.

Arthur Ezey
Bidiyoyin Biloniyan Najeriya Yana Rabawa Matasa $100 Kowannensu Ana Tsak da Karancin Kudi. Hoto daga @arthureze
Asali: Instagram

Mutane da dama sun ce biloniyan Anambra din yana sharar fage ne ga siyasarsa.

Wata mai amfani da kafar Twitter, @Firstladyship ce ta wallafa bidiyon, wanda ya jawo martani da dama , inda jama'a da dama suke ganin karamcin Eze na da nasaba da sharar fagen siyasarsa, yayin da wasu suka ruwaito yadda ya ke kokarin kauda talauci da tsananin rayuwar da karancin kudi suka jawo a Najeriya.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, ba a san adadin kudin da biloniyan ya kyautar ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Arthur Eze babban magoyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da dabarbarun tattalin arzikinsa, wanda mutane da dama suke ganin ya rage wa 'yan Najeriya da dama keburan talauci.

Inda suke ganin Eze na kokarin shawo kan tsananin rayuwar da jama'a ke fuskanta na karancin kudi.

Ta wannan fuskar, mutane da dama sun ce za a iya tuhumarsa da almundahanar kudi duba da dokar da ta haramta kashe kudaden ketare wadanda ba Naira da ake amfani da ita ba a kasar.

Martanin 'yan Najeriya

'Yan Najeriya sun yi martani game da bidiyon, inda wani ya kada baki ya ce biloniyan ya yi fice wajan hidimta wa al'umma.

"Wannan abun da ya saba ne faaa. Arthur Eze mai bayar wa ne. Ya kamata mu koyi hidimta wa al'umma daga gurinsa!"

Kara karanta wannan

Zabin Allah Na Bi: Bidiyon Soyayya Da Wata Kyakkyawar Mata Da Mijinta Mai Nakasa Ya Tsuma Zukata

@owolabitaiwo ya ce:

“Idan ka lura da kyautar Eze, za ka tabbatar da cewa akwai dollar a Najeriya fiye da naira.
"Idan ka yarda da hakan, ba tare da muhawara ba, dollar tafi naira yawa a Najeriya a halin yanzu."

@ninasteve007 ta ce:

"Ya kamata mu fara koya da hanzari daga wadannan 'yan siyasan. 1. Mai gina mutane, duk da haka baka da wani abu a kanka, ba za su zabeka ba! Don haka idan babu komai a kansu, KUMA KUY I WATSI DASU!
"2. Su na amsar kudi daga wurare amma BASA AMFANI DA SHI! ku ma, ku karbi kudin kuma ku karyar dasu!"

Keburan talauci: Matashi yace cocinsa ta dawo masa da duk sadakarsa

A wani labari na daban, wani matashi 'dan Najeriya yayi kira ga cocin Dunamis da ta dawo masa da duk sadakar da ya taba bayarwa.

Yace ya hakura da aljanna don shi yanzu wuta yake so, kuma ya da rasit din duk kudin da ya zuba musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel