EFCC: Ana zargin Ma’aikatan Prince Arthur Eze da laifin sace masa dukiya

EFCC: Ana zargin Ma’aikatan Prince Arthur Eze da laifin sace masa dukiya

- An yi wa fitaccen Attajirin nan, Prince Arthur Eze, satar makudan kudi

- Ana zargin wasu ‘yan gida daya ne da su kayi aiki da shi da wannan laifi

- EFCC tace kudin da aka sace daga hannun Attajirin sun haura Biliyan 1.5

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta gurfanar da wasu ‘yanuwan juna da laifin yi wa Prince Arthur Eze.

Ana zargin Eze Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka da kamfanoninsu da laifin satar N1.5b daga uban gidansu, Prince Arthur Eze.

A jawabin da hukumar EFCC ta fitar, ta nuna cewa an gurfanar da Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka a kotun tarayya da ke Abuja.

Lauyoyin EFCC su na zargin wadannan mutane da aka ce ‘yan gida daya ne da laifin yin sata.

KU KARANTA: Katafaren gidan da Neymar ya ke zama a Faris

EFCC ta jefi Okwuchukwu Olisaebuka da kamfaninsa na Berlus Resources Ltd da zargin aikata laifuffuka 17.

Daga cikin manyan laifuffukan da ake zargin wannan mutumi akwai satar N804, 360, 216.81 da $3,309,359.08 daga dukiyar ‘dan kasuwa Prince Eze.

Shi kuma Nnadozie Onyeka wanda shi ma ya yi aiki da attajirin, ana zargin cewa ya wawuri kudi N769, 161, 690, $845,700 da £80,200 daga hannunsa.

Duka wadannan mutane da ake zargi ba su amsa laifinsu ba, Alkali ya bada belin Okwuchukwu Olisaebuka a kan miliyan 10, Onyeka a kan miliyan 20.

EFCC: Ana zargin Ma’aikatan Prince Arthur Eze da laifin sace masa dukiya
Eze Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka Hoto: Twittter / @officialEFCC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wanda aka kama da laifin garkuwa da mai shekara 2 zai tafi kurkuku

Alkali mai shari’a ya dakatar da cigaba da sauraron wannan kara a ranar Laraba, ya sa ranar 26 ga watan Junairu, 2021, domin a fara gudanar da shari’a.

A yau ne mu ka tattaro maku jerin manyan gidajen attajiran da su ka fi kowane arziki a Duniya.

Zuri'ar Walton ce gida ko zuri'a mafi arziki a duniya a halin yanzu. Ana hasashen cewa kudinsu ya kai dala biliyan 215 kwatankwacin (₦81,958,000,000,000.02).

Wannan gida ne su ke da Walmart, kamfanin sari mafi yawan kudin shiga a duniya. Shaguna fiye da 11, 000 daga kasashen Duniya su ke yi wa kamfanin ciniki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel