Ana Tsaka da Batun Sauya Tsarin Mulkin Najeriya, Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Gana

Ana Tsaka da Batun Sauya Tsarin Mulkin Najeriya, Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Gana

  • Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma na yin taro a Gidan gwamnatn Legas da ke Ikeja watanni hudu bayan mutuwar Rotimi Akeredolu
  • Ana sa ran taron na kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma zai tattauna batutuwan da suka shafi shiyyar da ma Najeriya baki daya
  • Taron na zuwa ne yayin da ake sa ran shugaban kasa Bola Tinubu zai karbi kudurin sauya tsarin mulkin Najeriya a mako mai zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Rahotanni da ke shigo mana na nuni da cewa yanzu haka dai gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma na yin taro a Gidan Legas da ke Ikeja a jihar Legas.

Gwamnanonin Kudu maso Yamma sun gana a Legas
Legas: Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya karbi bakuncin gwamnonin Kudu maso Yamma. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

An ce gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya karbi bakuncin gwamnonin, wadanda suka dura Legas domin taron su na shiyyar a yau Litinin.

Kara karanta wannan

Ana tsananin rayuwa, an gano yadda gwamnoni suka kashe biliyoyi wajen sayan motoci

Gwamnonin Kudu maso Yamma sun gana

Gwamna Sanwo-Olu tare da mataimakinsa Dakta Obafemi Hazmat ne suka tarbi gwamnonin kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin da suka saka labulen su ne: Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Dapo Abiodun (Ogun), Seyi Makinde (Oyo), Ademola Adeleke (Osun) da Biodun Oyebanji (Ekiti).

Ana sa ran taron na kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma zai tattauna batutuwan da suka shafi shiyyar da ma Najeriya baki daya.

Taron na sirri wanda aka fara da misalin karfe 12:00 na rana na kan gudana a halin yanzu a ofishin Gwamna Sanwo-Olu da ke Gidan Legas, a Ikeja.

Batun zaben shugaban kungiyar gwamnonin

Legit Hausa ta ruwaito cewa taron na zuwa ne bayan watanni hudu da rasuwar shugaban kungiyar na karshe kuma tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

Bayan canja taken ƙasa, Tinubu zai karɓi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya

An ce Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun na shirin maye gurbin Akeredolu. Amma ana tunanin Seyi Makinde na jihar Oyo da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas na harin kujerar.

Duk da cewa gwamnoni shida na shiyyar sun yanke shawara a kan wanda zai zama shugaba, amma an ce Abiodun ya sanya kansa a cikin dabara domin ya zama shugaban.

Za a sauya kundin tsarin mulkin Najeriya?

Tun da fari, mun ruwaito cewa a mako mai zuwa ne ake sa ran shugaban kasa Bola Tinubu zai karbi wani kuduri da ke neman sauya tsarin gwamnatin Najeriya zuwa na 'Firmiya'.

Kudurin na ikirarin neman a rusa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda sojojin mulkin mallaka suka kakabawa kasar ba tare da la'akari da ra'ayin jama'a ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel