Ana Tsananin Rayuwa, An Gano Yadda Gwamnoni Suka Kashe Biliyoyi Wajen Sayan Motoci

Ana Tsananin Rayuwa, An Gano Yadda Gwamnoni Suka Kashe Biliyoyi Wajen Sayan Motoci

  • Gwamnoni sun sayi manyan motoci a yayin da yan Najeriya ke kokawa dangane da matsin rayuwa da kasar ke ciki
  • An gano yadda gwamnonin jihohi tara suka kashe makudan kudi sama da Naira biliyan 15 domin sayan manyan motoci
  • Bincike ya nuna cewa galibi an sayi motocin ne domin walwalar masu rike da madafun iko ba domin ayyukan cigaban jihohin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Binciken ya gano cewa gwamnonin jihohi tara a Najeriya sun kashe kudi sama da Naira biliyan 15 domin sayan motocin shiga.

Gwamnonin sun kashe kudin ne a lokacin da ake cikin matsin rayuwa da kuma bayyana cewa ba za su iya biyan kudin da kungiyar kwadago ke bukata a matsayin albashi ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun kashe yan sanda da mutane da asuba

Motocin yan majalisa
An kashe sama da N15b kan motocin yan majalisa a jihohi 9. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa daga cikin jihohin akwai Kano, Benue, Gombe, Ondo, Delta da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin da aka kashewa 'yan majalisar Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kashe kudi Naira biliyan 2.7 domin sayan motoci masu numfashi ga yan majalisar jihar.

Kowanne daya daga cikin yan majalisar jihar Kano ya samu mota da kimanin kudinta ya kai Naira miliyan 68.

Kudin motocin da aka kashe a Benue

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya sayi manyan motoci ga dukkan yan majalisun jihar Benue su 32.

Rahotanni sun nuna cewa kowacce mota da kowanne dan majalisa ya samu cikin su 32 ta kai kimanin Naira miliyan 60.

Kudin motcin da aka kashe Gombe

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya raba motoci 41 ga yan majalisun jihar da kwamishinoni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi albishir kan aikin jirgin kasan Legas zuwa Kano

Kudin ko wacce mota ya kai Naira miliyan 33.5. Gwamna Inuwa ya ce ya raba motocin ne domin saukaka ayyukan gwamnati.

Kudin da aka kashe a sauran jihohi

A jihar Kogi, an raba motoci 40 ga yan majalisa da alkalai. An raba motoci 21 a jihar Ondo wanda kowacce na kan N19m. Haka a jihar Ebonyi an raba guda 24 kowacce a kan N51m.

An kashe N19b a jihar Kebbi. An raba motoci 26 a jihar Osun. An raba motoci 25 a jihar Neja kowacce a kan N70m.

APC ta yi alwashin samun nasara

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana ƙwarin guiwar cewa za ta lashe zaɓen gwamnonin jihohin Ondo da Edo a 2024.

Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya ce idan Allah ya so za su fitar da Gwamna Obaseki da ƴan koransa daga gidan gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel