'Me Ma'aikata Za Su Yi da Albashin N62,000?' NLC ta yi Watsi da Sabon Tayin Gwamnati
- Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi watsi a tayin N62,000 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin mafi karancin albashi, karin N2000 daga tsohon tayin
- Mataimakin babban sakataren kungiyar, Chris Onyeka ya bayyana cewa ko N100,000 ba su kawo za su amince da shi ba ballantana N62,000 a yanayin tsadar da ake
- Zuwa yanzu NLC bata bayyana matakin gaba da za ta dauka ba, amma shugaban NLC reshen Kano Kwamred Kabiru Inuwa ya fadawa Legit suna dakon umarni daga sama
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Kungiyar kwadago ta caccaki gwamnati kan yi mata tayin N62,000 a matsayin mafi karancin albashi wanda ko kadan bai yi kusa da abin da ta nema ba.
Kungiyar ta ce ba ta amince da tayin N100,000 ba ma ballantana N62,000 a halin matsi da hauhawar farashi da 'yan Najeriya ke ciki.
Channels Television ta wallafa cewa mataimakin babban sakataren kungiyar, Chris Onyeka ne ya tabbatar da matsayar kungiyar kwadagon bayan gwamnati ta yi musu karin N2,000 a kan tayi na uku da ta yi masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
N250,000: NLC ta cimma matsaya kan albashi
Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana cewa ba ta za ta rage ko sisi daga N250,000 a matsayin mafi karancin albashi ba, kamar yadda The Cable ta wallafa.
Sabon kudin da NLC ta nema ya ragu matuka idan aka kwatanta da N694,000 da ta fitar a zamanta da kwamitin gwamnatin tarayya kan bukatarsu.
Mataimakin babban sakataren kungiyar, Chris Onyeka ya bayyana cewa kudin da su ka nema ba wai domin son rai ba ne, sai domin halin da farashin kayan amfani ya ke a kasuwanni.
'Muna jiran umarni daga sama' - NLC, Kano
Mataimakin sakataren kungiyar NLC na kasa, Chris Onyeka ya ce matukar gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace kan batun mafi karancin albashi ba, za su dauki mataki.
Da yake zantawa da Legit Hausa, shugaban kungiyar kwadago reshen Kano, Kwamred Kabiru Inuwa ya ce suna jiran umarnin mataki na gaba da NLC ta kasa.
Ya bayar da tabbacin kafin yau ta kare za su cimma matsaya ko dai na tafiya yajin aiki ko wanda uwar kungiyar ta ga ya dace.
Gwamnoni sun cimma matsaya kan albashi
A wani labarin kun ji cewa gwamnonin kasar nan sun yi taro kan mafi karancin albashi inda wata majiya ta ce ba za su iya biyan abin da ya haura N70,000 ba.
Gwamnonin na ganin akwai matsalar tattalin arziki wanda shi ne zai zame masu karfen kafa wajen biyan mafi karancin albashi fiye da aljihunsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng