Yan Sanda Sun Cafke Ɓarayin Mutane, Asirin Yan Bindigar da Suka Fitini Abuja Ya Tonu

Yan Sanda Sun Cafke Ɓarayin Mutane, Asirin Yan Bindigar da Suka Fitini Abuja Ya Tonu

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen birnin tarayya Abuja ta sanar da nasarar da ta samu bayan wani farmaki da ta kai kan yan bindiga
  • A cewar rundunar, ta kai farmakin ne cikin daji a wata maboyar masu garkuwa da mutane da ke tsakanin birnin tarayya da jihar Kaduna
  • Rundunar ta bayyana nasarar ta ta samu ciki har da kubutar da mutanen da aka kama da cafke manyan yan bindigan da suka fitini Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Rundunar yan sanda reshen birnin tarayya Abuja ta yi babban kamu yayin da ta kai farmaki kan yan bindiga.

A yayin farmakin, rundunar ta kama gungun yan bindigar da ake zargi da fitinar birnin Abuja da yawan garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Abuja, an kama miyagu

Yan sanda
Yan sanda sun kama yan bindigar da suka fitini Abuja. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

A wani bayani da rundunar yan sanda ta wallafa a shafin Facebook, ta sanar da cewa ta kai farmakin ne a wasu dazuka tsakanin jihar Kaduna da Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindigar da suka shiga hannu

Rundunar yan sanda ta sanar da cafke yan bindigan da suka hada da Yahaya Abubakar, Mohammed Mohammed, Umar Aliyu da Nura Abdullahi.

Yan bindigar sun amsa laifinsu kuma sun bayyana cewa sune ke jagorantar gungun masu garkuwa da mutane da ake kira da 'Mai One Million' a Abuja.

Sun kuma bayyana cewa su ne suka hana birnin tarayya da yankunanta zaman lafiya saboda tsananin sace-sace.

Yadda aka kama yan bindigar a jeji

Rundunar yan sanda ta yi haɗaka da jami'an DSS, sojoji da yan farauta kafin kai farmaki kan yan ta'addan a jejin Gidan Dogo da Kweti.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Isan jami'an tsaron ke da wuya aka fara musayar wuta tsakaninsu da yan bindigar wanda daga baya hukumomi suka yi nasara.

Hakan yasa yan sanda suka kubutar da wadanda aka sace tare da rusa sansanin yan bindigar a jejin.

Yan sanda sun kama Chinaza Phillip

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Chinaza Phillip bayan musayar wuta.

Rahoto ya nuna dakarun ƴan sanda sun yi gumurzu da mayaƙan Phillip kafin daga bisa su yi nasarar kama shi da kubutar da wani mutum ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel