Gwamna Zulum Ya Mika Mulkin Jihar Borno Ga Mataimakinsa, Ya Fadi Dalili

Gwamna Zulum Ya Mika Mulkin Jihar Borno Ga Mataimakinsa, Ya Fadi Dalili

  • Daga ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, jihar Borno ta samu sabon wanda zai jagoranci gudanar da mulkinta na tsawon kwanaki 28 masu zuwa
  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya miƙa ragamar mulkin jihar Borno ga mataimakinsa watau Umar Usman Kadafur
  • Gwamna Zulum wanda wannan shi ne karo na biyu da yake miƙa mulki ga mataimakinsa, ya tafi Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa Umar Usman Kadafur.

Gwamna Zulum ya miƙa mulkin ne domin tafiyar ƙasar Saudiyya gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Gwamna Zulum ya mika mulki ga mataimakinsa
Gwamna Zulum ya tafi Saudiyya aikin Hajji Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Zulum ya bi sahun Alhazan Borno 1,815 da ke a ƙasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yiwa Alhazan jihar babban gata a Saudiyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum ya miƙa mulki a Borno

A wani zaman gaggawa da aka yi a ranar Juma’a, kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Honarabul Abdulkareem Lawan, ya bayyana cewa gwamnan ya tafi hutun kwanaki 28, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

A cewar kakakin majalisar, mataimakin gwamnan ne zai jagoranci harkokin mulki daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 8 ga watan Yuli, 2024.

Doka ta ba Zulum damar mika mulki

Ya yi nuni da cewa matakin miƙa mulkin ya yi daidai da tanadin sashe na 190 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce amincewar majalisar za ta ba mataimakin gwamnan cikakken ikon tafiyar da al’amuran jihar ba tare da jiran gwamnan ba.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Gwamna Zulum ya miƙa mulki ga Umar Usman Kadafur domin ya zama gwamna.

Kara karanta wannan

Sallah: Bayan Dikko Radda na Katsina, gwamnan Sokoto ya yi abin alkairi ga ma'aikata

Zulum ya je Saudiyya a 2021

Karo na farko shi ne a watan Afrilu, 2021 lokacin da Gwamna Zulum ya tafi hutu na kwanaki 21.

Ya shiga jirgi na ƙarshe na Alhazai 175, wanda ya tashi da misalin ƙarfe 2:35 na dare a filin jirgin saman Maiduguri, sannan sauka a filin jirgin Yarima Mohammed bin Abduaziz da ke Madina da ƙarfe 8:10 na safe.

Gwamna Zulum ya ba da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya kaddamar da shirin mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu a kananan hukumomi tara da ke jihar.

Bugu da ƙari, Gwamna Zulum ya rabawa waɗanda za a mayar gida N954.7m domin su farfaɗo da sana'o'insu kuma su samu abubuwan dogaro da kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng