Bayan Canja Taken Ƙasa, Tinubu Zai Karɓi Ƙudurin Sauya Tsarin Mulkin Najeriya

Bayan Canja Taken Ƙasa, Tinubu Zai Karɓi Ƙudurin Sauya Tsarin Mulkin Najeriya

  • A mako mai zuwa ne ake sa ran Shugaba Bola Tinubu zai karbi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya zuwa 'gwamnatocin shiyya'
  • Dan majalisar wakilai, Dr. Akin Fapohunda ne ya gabatar da kudurin kuma ya sha alwashin mikawa Tinubu ko da majalisa ba ta so
  • A baya majalisar wakilai ta nesanta kanta da wannan kuduri, amma Fapohunda ya dage kan cewa shugaban kasar zai yi maraba da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A mako mai zuwa ne ake sa ran Shugaba Bola Tinubu zai karbi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya zuwa 'gwamnatocin shiyya na Firimiya.'

Idan har shugaban kasar ya sa hannu kan wannan kudiri, shiyyoyin Najeriya za su zama karkashin 'Firimiya' kamar yadda aka yi kafin juyin mulkin soja.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa Bola Tinubu ya fi Atiku da Obi cancantar zama shugaban ƙasa a 2023"

Tinubu zai karbi kudurin sauya mulkin Najeriya
Mako mai zuwa Tinubu zai karbi kudurin sauya tsarin mulkin Najeriya. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ruwaito ɗan majalisar wakilai, Dr. Akin Fapohunda ya sha alwashin mika kudurin dokar ga Shugaba Tinubu a mako mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da kudurin dokar ya kunsa:

1. Taken kudirin sauya tsarin mulkin

Taken kudirin dokar shi ne: "Kudirin sauya dokar sojoji mai lamba 24 ta 1999 zuwa ga sabon tsarin gwamnati a Tarayyar Najeriya."

2. Sabon sunan kundin tsarin mulkin Najeriya

Kudirin ya nemi a rika kiran dokar: "Kundin tsarin mulkin Najeriya na sabuwar gwamnati ga Najeriya da aka sabunta a 2024."

3. Rusa kundin mulkin Najeriya na 1999

Kudirin dokar ya ce:

"Za a rusa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda sojojin mulkin mallaka suka kakabawa kasar ba tare da la'akari da ra'ayin jama'a ba."

4. 'Yan Najeriya na neman sauyin tsarin mulki

Har ila yau, kudurin dokar da za a gabatar wa Tinubu ya yi nuni da cewa:

Kara karanta wannan

Kudurin ƙirƙirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas ya wuce karatun na 1 a majalisar wakilai

"Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ba ya a kan tafarkin muradun jama'a, kuma yanzu lokaci ne da 'yan kasa ke bukatar a koma tsarin gwamnatin shiyya."

5. Shiyyoyin Najeriya za su samu 'yanci

Kudirin dokar na neman a koma tsarin gwamnatin shiyya, ta yadda jihohin da ke a karkashin shiyya daya za su rika tafiyar da ragamar lamuran su ba tare da cikas ba.

Kudurin na nufin ganin cewa an koma yadda tsarin 'firimiya' kamar yadda aka yi a zamanin su Abubakar Tafawa Balewa, inda kowacce shiyya ke da na ta ikon gwamnati.

Majalisar wakilai ta yi fatali ƙudurin

A karshen watan Mayun 2024, jaridar The Cable ta ruwaito majalisar wakilai ta yi fatali da wannan kudiri na sauya tsarin mulkin Najeriya zuwa gwamnatin shiyya.

Mai magana da yawun majalisar wakilai, Yemi Adaramodu ya ce wannan kudirin dokar wanda har ya fara yawo a intanet bai fito daga zauren majalisar ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu a faifayi: Ko ya cika manyan alkawuran da ya yi a cikin shekara 1?

Haka zalika, Hon. Akin Rotimi da Hon. Francis Waive sun nesanta majalisar da wannan kudiri suna masu cewa kudurin bai je ga kwamitin tantance wa na majalisar ba.

Mako mai zuwa Tinubu zai karɓi ƙudurin

Sai dai duk da majalisar ta ki karbar kudirin, Dr. Akin Fapohunda wanda ya gabatar da kudirin ya lashi takobin mika wa shugaban kasa kudurin a mako mai zuwa.

Dr. Fapohunda ya yi nuni da cewa idan har Shugaba Tinubu ya duba kudirin, yana kyautata zaton zai gabatar da shi ga majalisa matsayin kudirin shugaban kasa na kai tsaye.

Kansilan Kano ya yiwa marayu gata

A wani labarin, mun ruwaito cewa kansila mai wakiltar gundumar Achika ta karamar hukumar Wudil a jihar Kano, Bashir Aliyu, ya dauki nauyin karatun yara marayu 120.

A wani bikin bayar da kayayyakin karatu ga yaran da aka gudanar a gundumar Achika a ranar Lahadi, Hon. Aliyu ya ce ya yi hakan domin gyara makomar marayun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel