Gwamnatin Jihar Delta Ta Haramta Yin Acaba, ’Yan Arewa Za Su Dawo Gida
- Gwamnatin jihar Delta ta haramta yin acaba a fadin jihar domin dakile yawaitar ta'addancin da ake yi da baburan
- Rundunar 'yan sandan jihar ta ce za ta tsaurara matakai kan hana yin acaba kuma ba za a daga kafa ga masu karya doka ba
- Bayan kakaba wannan doka, an fara fargabar 'yan Arewa da ke yin kabu kabu a jihar yanzu za su dawo gida ko su canja sana'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Delta - Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Bright Edafe, ya ce dokar hana yin acaba da aka fi sani da Okada na nan daram.
'Yan sun gargadi 'yan acaba a Delta
Ya gargadi 'yan acaba da su sanya wa baburan su kwado su kulle domin gwamnatin jihar Delta ta ba da umarnin murkushe duk wani babur din da aka kama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edafe ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Ya wallafa cewa:
“Dokar hana yin acaba ta nan daram kuma za mu tabbatar an aiwatar da ita. Yana da kyau 'yan acaba su boye baburansu domin 'Edafe Bright' ba zai iya kawo dauki idan muka kama shi ba."
Gwamnatin Delta ta haramta acaba
Sakataren gwamnatin jihar, Kingsley Emu ne ya sanar da haramta acaba a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar 24 ga watan Mayu.
A cewar Emu, haramta acaba a ya zama dole saboda karuwar laifuffukan da ake yi da baburan da kuma yawaitar barnar da ake samu a jihar, in ji rahoton jaridar The Punch.
Ana fargabar 'yan Arewa za su dawo gida
Bayan kakaba wannan doka ta hana acaba, an fara fargabar 'yan Arewa da ke yin kabu kabu a jihar yanzu za su dawo gida ko kuma su canja wata sana'ar domin bin doka.
A mafi yawan jihohohin Kudu da aka haramta yin acaba, 'yan Arewa da ke kwadago a wajen ne abin ya fi shafa, musamman wadanda sana'ar acabar ce dama ta kai su.
An haramta yin acaba a Calabar
A wani labarin, mun ruwaito Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Ribas ya haramta yin acaɓa a cikin kwaryar birnin Calabar, babban birnin jihar.
Gwamnatin jihar Cross River ta kuma gargaɗi jama'a cewa duk wanda ta kama ya karya wannan doka zata kwace Babur ɗinsa kuma zata gurfanar da shi a gaban kotu.
Asali: Legit.ng