Sojoji sun gasa wa 'yan Boko Haram aya a hannu a Maiduguri
Dakarun Sojojin Najeriya sun dakile harin da mayakan Boko Haram suka kai garin Maiduguri kamar yadda wata majiya daga jami'an tsaro da mazauna garin suka shaidawa AFP.
Harin yana daya daga cikin hare-haren da mayakan kungiyar ta'addar su kayi yunkurin kaiwa amma sojoji suka dakile harin sa'o'i kadan kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa a zango na biyu.
Sojojin sunyi artabu da mayakan Boko Haram masu yawa a wajen garin Maiduguri a daren Talata inda suka kwana fafatawa har zuwa asubahin ranar Laraba.
DUBA WANNAN: Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu
"Sojojin mu sunyi bajinta sun fattaki 'yan ta'addan," inji wata majiyar sojoji da ya bukaci a sakaya sunansa.
Sojojin sunyi ta fafatawa da su tsawon dare kuma suka tilasta su tserewa da asuba inji majiyar.
Wani dan kungiyar sa kai da ke yaki tare da sojojin ya ce an gano mayakan Boko Haram a yayin da suke kokarin zuwa garin da dare.
"Anyi sa'a cewa sojojin sun gan su kuma suka yi artabu da su tsawon dare," inji shi.
Mazauna garin sun ce sun ji karar bindigu a cikin dare.
"Muna ta jin karar bindigu cikin dare," inji wani mazaunin garin mai suna Nasiru Fannami.
A yanzu dai ba a sani ko akwai wadanda suka rasu ba.
Mayakan Boko Haram sunyi ta yunkurin kai hari a Maiduguri amma ba su yin nasara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana
Asali: Legit.ng