'Yan Kwadago Na Shirin Ɗaukar Mataki Bayan Gwamnatin Tinubu Ta Miƙa Tayin N62,000
- Alamu na nuna abu ne mai wahala ƴan kwadago su amince da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata
- Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa ya ƙarƙare tattaunawa kuma ya faɗi adadin kuɗin da yake ganin za su inganta rayuwar ma'aikata
- Sai dai har yanzun NLC ba ta ce komai ba duk da ƴan kwadagon sun rage bukatarsu daga N494,000 zuwa N250,000
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi ya ƙarƙare zaman tattaunawa a ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, 2024.
Bayan shafe sa'o'i ana tattake wuri, kwamitin ya bayar da shawarin N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.
Jaridar Leaderhship ta tattaro cewa ƴan kwadago sun yi fatali da sabon tayin, inda suka jaddada cewa sun rage bukatarsu zuwa N250,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun amince da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
NLC ka iya komawa yajin aiki
Da alamu dai rashin jituwar na iya tilastawa kungiyoyin kwadago NLC da TUC, su sake farfado da yajin aikin da suka sassauta na mako guda.
NLC na duba yuwuwar sake komawa yajin aikin wanda ta ɗage na tsawon kwanaki biyar bayan gwamnati ta tsaya kan sabon tayin.
Idan baku manta ba a baya gwamnatin tarayya ta gabatar da tayin N60,000 wanda ya fusata ƴan kwadago suka fice daga taron.
Suka kuma ayyana shiga yajin aiki kan gazawar gwamnati game da ƙarin albashi da kuma ƙarin kuɗin wutar da aka yiwa ƴan rukunin Band A, The Cable ta ruwaito.
Bayan haka a ranar Talata, Shugaban kasar ya umarci Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun, da ya tsara tsarin mafi karancin albashi na kasa cikin sa'o'i 48.
Sai dai har zuwa daren ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, ana ci gaba da dakon martanin ƙungiyar kwadago a hukumance kan sabon mafi ƙarancin albashin.
Gwamnoni ba zasu iya biyan N60,000 ba
A wani rahoton ƙungiyar gwamnoni 36 na Najeriya (NGF) ta ce mambobinta ba za su iya biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ba.
Mai magana da yawun NGF, Hajiya Halima Salihu ta ce kuɗin sun yi yawa kuma gwamnoni ba za su iya jure biya ba.
Asali: Legit.ng