InnalilLahi: Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi Bayan Rasuwar Babban Limamin Borno
- Tsohon babban limamin jihar Borno, Imam Asil Adam ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar jinya
- Marigayin Asil Kyari ya rasu ne da yammacin yau Juma'a 7 ga watan Yuni a birnin Maiduguri da ke jihar
- Legit Hausa ta ji bakin daya cikin ƴaƴansa kan wannan babban rashi da suka yi na wannan malami a jihar Borno
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - An shiga jimami bayan rasuwar tsohon babban limamin jihar Borno, Imam Asil Adam Kyari da yammacin yau.
Marigayin Imam Asil ya rasu ne da yammacin yau Juma'a 7 ga watan Yuni a birnin Maiduguri da ke jihar.
Borno: Babban limamin ya rasu bayan jinya
Imam Asil ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya, kamar yadda rahoton Zagazola Makama ya tabbatar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutuwar babban limamin ga girgiza mutane da dama inda suka bayyana limamin a matsayin mutumin kirki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa za a gudanar da sallar jana'izarsa a gobe Asabar 8 ga watan Yuni a gidansa da ke "Limanti kura" Gamboru kasuwan shanu a birnin Maiduguri da misalin karfe 2:30 na rana.
Tattaunawar Legit Hausa da ɗan malamin
Legit Hausa ta ji bakin daya cikin ƴaƴansa kan wannan babban rashi da suka yi na wannan malami.
Abdul K Imam ya ce tabbas sun yi babban rashin mutumin kirki inda ya ce marigayin a matsayin kawunsa ya ke.
"Marigayi Imam mutumin kirki ne, mai addini sosai kuma dabi'arsa ce ya kyautatawa gajiyayyu."
"Ya koyar da mu kuma mun koyi abubuwa da dama daga wajensa, Alhamdulillah."
- Abdul K Imam
Farfesa a Jami'ar Maiduguri ya rasu
Har ila yau, a jihar Borno, an sanar da mutuwar fitaccen Farfesa a Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.
Marigayi Farfesa Mustapha Kokari da ke tsangayar halittu ya rasu ne a ranar Asabar 18 ga watan Mayun wannan shekara da muke ciki.
Matashin makamin Musulunci ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa matashin mai da'awar Musulunci, Abdullateef Aliyu Maitaki ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.
Marigayin wanda aka fi sani da Mufti Yaks ya kasance yana kwaikwayon fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Isma'il Ibn Menk (Mufti Menk).
Asali: Legit.ng