Matasan Bauchi Sun Yi Ajalin Yunusa Kan Zargin Furta Kalaman Batanci ga Annabi SAW

Matasan Bauchi Sun Yi Ajalin Yunusa Kan Zargin Furta Kalaman Batanci ga Annabi SAW

  • An shiga wani irin yanayi a jihar Bauchi bayan wasu matasa sun yi ajalin matashi kan zargin kalaman ɓatanci
  • Ana zargin Yunusa wanda ɗan Faira ne da furta kalamai marasa daɗi ga Annabi Muhammad (SAW) a jihar
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Nasaru da ke karamar hukumar Bauchi a jiya Laraba 19 ga watan Yunin 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Wasu matasa sun yi ajalin wani a jihar Bauchi kan zargin batanci ga fiyayyen halitta.

Matasan sun yi ajalin matashin ne mai suna Yunusa a kauyen Nasaru da ke karamar hukumar Ningi a jihar.

An hallaka wani matashi a Bauchi kan batanci ga fiyayyen halitta
Matasa a jihar Bauchi sun hallaka wani kan zargin furta kalaman batanci ga fiyayyen halitta.
Asali: Original

Bauchi: An kashe rai kan kalaman batanci

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, miyagu sun yi ta'asa har da jikkata yan sanda

Lamarin ya faru ne a jiya Laraba 19 ga watan Yunin 2024 kan zargin kalamai marasa daɗi ga Annabi Muhammad (SAW) a cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yunusa kamar yadda shaidun gani da ido suka fada ya furta kalaman ne yayin da suke gardama mai zafi, Sahara Reporters ta tattaro.

Abin da ya yi sanadiyyar kashe Yunusa

"Yunusa ya kasance ɗan Faira ne, ya furta wasu malamai da ba su dace ba, inda aka bukaci ya janye ya ki, har aka fara dukansa."
"Bayan bukatar ya janye kalaman nasa sai ya ki tare da maimaita su daga nan ne mutane suka farmasa."

- Cewar majiyar

Wane yunkuri ƴan sandan Bauchi suka yi?

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan sanda sun yi kokarin cetonsa amma mutane sun fi karfinsu inda suka yi amfani da sanduna da duwatsu wurin hallaka shi.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

An ruwaito cewa matasan sun yi kokarin kona ofishin ƴan sanda a kauyen bayan jami'an sun yi yunkurin dakatar da su.

An hallaka matashi kan batanci a Sokoto

A baya kun ji cewa fusatattun matasa sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Lamarin ya faru ne a babban mayanka ta jihar Sokoto da safiyar ranar Lahadi 25 ga watan Yunin 2023 da misalin karfe 8:00 na safe.

Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa marigayin yana zama ne a Gidan Igwe da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.