NSCDC a Kano ta Damke Masu Addabar Al'ummar Jihar da Sace Sace

NSCDC a Kano ta Damke Masu Addabar Al'ummar Jihar da Sace Sace

  • Hukumar tsaron fararen hula ta reshen Kano ta cafke wasu matasa biyar da ake zargi da barnatar da kayan jama'a da satar babura a wasu sassan jihar
  • Kwamandan hukumar Mohammad Lawal-Falala ne ya shaidawa manema labarai hakan ta cikin sanarwar da kakakinta, Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar
  • An kama matasa biyu da kokarin cire fitilun kan titi, yayin da sauran matasa uku mazauna unguwar Gwammaja aka kama su bisa zargin satar babura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Rundunar tsaron fafaren hula (NSCDC) reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da barnatar wayoyin fitilun kan titi a yankin karamar hukumar Fagge.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

Wadanda aka kama sun hada da wani Adnan Umar, mai shekara 26, da Musa Shu’aibu, mai shekara 24, kamar yadda kwamandan hukumar Mohammad Lawal-Falala ya bayyana.

NSCDC
NSCDC ta damke matasa biyar bisa zargin lalata kayan amfanin al'umma Hoto: Nigeria Security and Civil Defence Corps
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa kwamandan, Mohammad Lawal-Falala ta cikin sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar ya ce an kama bata-garin ne da tsakar dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NSCDC ta kama barayin babur

Hukumar NSCDC a Kano ta bayyana cafke wasu matasa uku da zargin satar babur da suka hada da wani Saminu Magaji, Haruna Idris da Ahmad Abubakar.

Daily Trust ta wallafa cewa dukkanin matasan mazauna Gwammaja ne da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano.

Hukumar NSCDC ta kara da cewa baya ga satar babur, ana zargin matasan sun dade suna haurawa gidajen jama'a su sace babura da sauran kayan amfani.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Niger ta bayyana abin da ke kawo cikas wajen ceto wadanda gini ya rufta musu

Yanzu haka dai kwamanda Mohammad Lawal-Falala ya ce ana zurfafa bincike kan matasan biyar da aka kama, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an gama.

NSCDC ta kama masu safarar mutane

A wani labarin kun ji cewa hukumar tsaron fararen hula ta kasa (NSCDC) a jihar Kano ta damke wasu da ake zargi da safarar mutane zuwa kasashen ketare.

Hukumar ta bayyana cewa an ceto wasu mutane 14 da ake niyyar fita da su zuwa kasar Kamaru ta iyakar Maidguri domin ci rani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel