An Fallasa Yadda Gwamnonin Jihohi Suka Kashe N960bn Domin Walwala a Watanni 3

An Fallasa Yadda Gwamnonin Jihohi Suka Kashe N960bn Domin Walwala a Watanni 3

  • Alkaluma sun gano yadda gwamnatocin jihohin Najeriya suka kashe wasu makudan kudade da yawansu ya kai N986.64bn domin walwala da jin dadinsu
  • An yi amfani da kudin wurin sayawa baki kayan taba-ka-lashe, da kudin alawus na zaman taro ga jami'an gwamnati, sai biyan kudin ruwa da wuta
  • Jihohi 30 ne aka tabbatar sun hadu wajen kashe adadin kudin cikin watanni ukun farkon shekarar 2024 yayin da ake kokarin cimma matsaya kan albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria- Bincike ya fallasa yadda gwamnatocin jihohin kasar nan 30 suka kashe makudan kudi wajen sayen kayan kwalam da makulashe yayin taro, da tafiye-tafiyensu cikin watanni uku.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

An gano cewa a cikin watanni uku kacal, gwamnonin sun kashe N986.64bn domin walwalarsu yayin gudanar da tarurruka.

Gwamnatocin jihohi
Jihohin kasar nan sun kashe N968.64bn domin walwalarsu cikin watanni 3 Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar Punch News ce ta tattaro alkaluman ta hanyar amfani da bayanan da shafin BudgIT ke wallafawa wanda ke dauke da bayanan kudin ga gwamnatoci ke kashewa a jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnoni 30 suka kashe N986.64bn

Rahotanni sun gano cewa jihohin sun kashe N5.1bn wajen sayawa baki abin makulashe, inda aka batar da N4.67bn a matsayin alawus na zama ga jami’an gwamnati.

Haka kuma an kashe wasu N34.63bn kan tafiye-tafiye, da wasu N5.64bn da aka kashe domin biyan kudin wuta da ruwa.

Wasu miliyoyin sun tafi ga kudin hawa yanar gizo, zubar da shara da makamantansu, kamar yadda News Now Nigeria ta wallafa.

Gwamnonin Jihohin da suka batar da N986.64bn

Ga jerin jihohin kasar nan da adadin da suka kasha a watanni ukun farkon shekarar nan;

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe za ta yi titin da kilomita 1 zai lakume sama da Naira biliyan 1

1.Adamawa -N23.7bn

2.Akwa Ibom -N46.85bn

3.Anambara -N9.91bn

4.Bauchi - N35.75bn

5.Bayelsa- N35.1bn

6.Lagos N189.62bn

7.Borno N18.79bn,

8.Jigawa N15.52bn

9. Kaduna N34.69bn

10. Kano N34.41bn

11. Katsina N21.87bn,

12. Kebbi N11.67bn

13. Kogi N37.4bn,

14. Kwara N24.34bn,

15. Nasarawa N18.61bn

16. Ogun N47.12bn

17. Ondo N31.12bn

18. Osun N24.39bn

19. Oyo N40.12bn

20. Plateau N24.70bn

21. Zamfara N13.46bn

22. Taraba N20.93bn

23. Abia- N10.92bn

24.Cross Rivers N17.44bn

25.Delta N68.68bn

26.Ebonyi N14.95bn

27. Edo N32.32bn

28. Ekiti N32.8bn

29. Enugu N7.51bn

30. Gombe N20.89bn

Hanyoyin samun kudi sun yi karanci a Kaduna

A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin jihar Kaduna na fuskantar barazana saboda karancin hanyoyin samun kudin shiga bayan tafiyar gwamnatin Nasir El-Rufa'i.

Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar, Jerry Adams da ya bayyana damuwar ya kuma ce gwamnati ta kaddamar da sababbin hanyoyin tattara kudin haraji domin magance matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel