Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Fitaccen Dan TikTok, G Fresh Al'ameen, an Gano Dalili
- Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa hukumar Hisbah ta Kano ta kama fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al'ameen
- An ce hukumar ta kama mawakin ne bayan tarin gargadi da ta yi masa kan kalamai, rawa da bidoyon batsa da ya ke yadawa
- Haka zalika, ana zargin G-Fresh Al'ameen da yin izgili ga ayoyin Al-Kur'ani, wanda za a gurfanar da shi gaban kotu a gobe Litinin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al'ameen saboda zargin yi wa Al-Kur'ani izgili.
Babban daraktan Hisbah na jihar, Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar da kama G-Fresh ga manema labarai a ranar Lahadi.
Shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito cewa hukumar ta kama fitaccen dan TikTok din ne bayan bijirewa gargadin da ta yi masa kan abubuwan da ya ke ɗora a intanet.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Sufi ya ce:
"Mun kama G-Fresh Al'ameen ne bayan tarin gargadi da muka yi masa kan abubuwan badala da ya je wallafawa a TikTok da sauran shafukan sadarwa."
Hukumar ta Hisbah ta ce za ta gurfar da G-Fresh a gaban kotu a gobe Litinin, 3 ga watan Yuni.
Wani rahoto da shafin rediyon Freedom na Kano ya fitar, ya nuna cewa Husbah ta kama G-Fresh saboda yin izgili ga ayoyin Al-Kur'ani.
Haka zalika, ana zargin fitaccen dan TikTok din, wanda kuma mawaki ne da furta kalamai da rawar batsa a soshiyal midiya.
Hisbah ta kama fitacciyar 'yar TikTok
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama kama shahararriyar jarumar TikTok, Ramlat Princess kan zargin tallata madugo a cikin al'umma.
Hukumar Hisbah a Kano dai na ci gaba da kai samame kan masu yada badala da dabi'un rashin tarbiya a shafukan soshiyal midiya musamman ma TikTok.
Asali: Legit.ng