Tsohon Sanatan Katsina Ta Kudu, Abu Ibrahim Ya Kwanta Dama? Iyalansa Sun Magantu
- Jita-jita ta karade kafofin sada zumunta cewa tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina ta Kudu, Sanata Abu Ibrahim ya rasu
- A wata sanarwa da dansa, Muhammad Abu Ibrahim ya fitar, iyalan Sanata Ibrahim sun karyata wannan jita-jitar tare da yin karin haske
- Muhammad Abu Ibrahim, ya ce wannan jita-jita ba gaskiya ba ce, kasancewar mahaifinsa na raye kuma cikin koshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Funtua, Katsina - Iyalan Sanata Abu Ibrahim, tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina ta Kudu, sun karyata rade-radin da ake yadawa cewa dattijon ya rasu.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da dansa, Muhammad Abu Ibrahim, shugaban hukumar tallafawa harkar noma ta kasa (NADF), ya fitar a madadin iyalan.
Muhammad Abu Ibrahim, ya ce wannan jita-jita ba gaskiya ba ce, kasancewar mahaifinsa na raye kuma cikin koshin lafiya, in ji rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Abu Ibrahim bai mutu ba
A cewar sanarwar:
“An ja hankalinmu kan jita-jitar mutuwar mahaifinmu kuma mai fada a ji a jiharmu, Sanata Abu Ibrahim, da aka fara yadawa a ranar Asabar, 1 ga Yuni, 2024.
“Muna son bayyana cewa wannan jita-jitar da ake yadawa ba gaskiya ba ce; Sanata Abu Ibrahim yana raye kuma yana cikin koshin lafiya.
“Muna matukar godiya ga wadanda suka rika bugo waya ko zuwa takanas har gida domin tabbatar da wannan jita-jitar la'akari da damuwar da shuga shiga."
Tsohon mai neman takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya wallafa sanarwar a shafinsa na X.
Abin sani game da Sanata Abu Ibrahim
An zabi Abu Ibrahim a matsayin sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu (shiyyar Funtua) a watan Afrilun 2003 a karkashin jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
A Agusta 2006, a ka kore shi daga ANPP, kamar yadda aka kori tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi ma daga Katsina. An zarge su da yi wa jam'iyya zagon kasa.
Sanata Ibrahim ne ya taka rawar gani a hadewar jam'iyyar CPC da AC da kuma taka rawa a alakar Bola Tinubu na AC da Muhammadu Buhari na CPC.
Ibrahim ya zama mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa tsakanin 2011 zuwa 2015.
Matar aure ta haifi 'yan 4 reras
A baya, mun ba da labarin wata mata da ta haifi 'yan hudu reras bayan shafe shekaru 18 da yin aure ba tare da ta taba yin ko da bari ba.
'Yan uwa, abokan harziki da ma ma'abota shafukan yanar gizo sun cika da farin ciki bayan wannan matar wadda ‘yar Najeriya ce ta samu karuwa.
Asali: Legit.ng