Buhari zai ci koda kuwa babu nPDP - Sanata Abu Ibrahim
A jiya ne Sanata Abu Ibrahim (APC katsina), yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai lashe zaben 2019 koda akwai, ko babu 'yan sabuwar jam'iyyar nPDP
A jiya ne shugaban kwamitin kula da al'amuran hukumar 'yan sanda na majalisar dattawa, Sanata Abu Ibrahim (APC katsina), yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai lashe zaben 2019 koda akwai, ko babu 'yan sabuwar jam'iyyar nPDP.
Ibrahim, wanda shine shugaban Buhari Support Group (BSG), ya karyata ikirarin da 'yan nPDP suke na cewa sunfi kowa taka rawar gani a nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben 2015.
DUBA WANNAN: Shehu Sani: Zan fito takarar gwamnan Kaduna, kuma zan kada El-Rufai
Yayi maganar ne a tataunawa da akayi dashi sakamakon jita jitan da 'yan nPDP, wanda ya hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, suke yadawa zasu bar jam'iyyar ta APC.
"Siyasa ai siyasa ce. Zabe yana zuwa ; sunan PDP gawa tun ranar da 'yan jam'iyyar suka koma APC. 'yan Najeriya kada su dauka cewa akwai wata sabuwar nPDP kamar yanda babu ACN, CPC. " inji shi.
Ibrahim yace tashin tashinar da 'yan sabuwar jam'iyyar nPDP suke tadawa, sunayi ne kawai don rashin nasarar da suke hangowa a zaben 2019 da ke tunkarowa.
"APC zatayi nasara ko akwai, ko babu 'yan sabuwar jam'iyyar ta nPDP ; zamu jajirce kuma zamuyi nasara. Na musanta zancen su na cewa su ne suka tsaya, tsayin daka don ganin nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015. A takaice ma akwai wani dan sabuwar jam'iyyar ta nPDP da ya roki shugaban kasa da yayi mishi kamfen a shekarar 2015 din a jihar Gombe."
Ya kara da cewa kokarin da shugaban kasar yayi a bangarori da dama, wanda ya hada da tattalin arziki, ya kara fito da martabar shugaban kasar har a kasashen ketare.
"Idan mutum marar son zuciya ya zagaye kasar nan, zai ga abubuwan da gwamnatin tayi. Nasan shugaban kasa Muhammadu Buhari sosai, mutum ne mai nagarta. Bazai bari ayi magudin zabe ba. 'yan sabuwar jam'iyyar nPDP hassada ke damunsu."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng