Buhari ya yi wata ganawar sirri da Sanata Abu Ibrahim da Gwamna Masari

Buhari ya yi wata ganawar sirri da Sanata Abu Ibrahim da Gwamna Masari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wata ganawar sirri da gwamnan jahar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, tare da Sanatan yankin karaduwa, Sanata Abu Ibrahim a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito har zuwa lokacin tattara rahoton nan shuwagabannin uku suna cikin wannan ganawa a fadar shugaban kasa, ganawar da suka fara tun da misalin karfe 2 na rana.

KU KARANTA: Ranar kin dillanci: Jami’an EFCC sun shirya ma gwamnan jahar Ekiti tarkon rago

Majiyarmu ta kara da cewa Sanata Abu Ibrahim ne ya fara isa fadar shugaban kasa da yan mintuna, kafin gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari shima ya isa fadar, daga nan suka rankaya zuwa ofishin shugaban kasa.

Sanata Abu Ibrahim shine shugaban kwamitin kula da al’amuran Yansandan Najeriya a majalisar dattawa, sai dai Sanata ba shi da sha’awar sake neman kujerar da yake kai, don haka ya kaurace ma zaben fidda gwani na Sanatocin jahar Katsina.

Sai dai masana al’amura siyasar jahar Katsina sun ce an gudu ne ba’a tsira ba, saboda Abu Ibrahim na da hannu cikin fitar da dan takarar kujerar Sanatan yankin karaduwa da ya lashe zaben fidda gwani, Mandiya.

Alakar dake tsakanin Abu Ibrahim da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba boyayya bace, inda Abu Ibrahim ya bayyana cewa Buhari maigidansa ne tun a makarantar sakandari, don haka a yanzu hakaake ganin tunda dai ya fasa tsayawa takarar Sanata, Buhari zai iya nada shi wani muhimmin mukami.

A wani labarin kuma, gidan rediyon muryar Amurka, VOA, ta salami ma’aikatanta su goma sha biyar a sanadiyyar karbar kudin goro da suka yi daga gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, kudin da suka kai dala dubu biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng