‘Yan Najeriya Sun Zabi Ministocin da Za a Kora da Wadanda Tinubu Zai Bari a Ofis

‘Yan Najeriya Sun Zabi Ministocin da Za a Kora da Wadanda Tinubu Zai Bari a Ofis

  • A watan Mayu Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara guda yana a matsayin shugaban Najeriya mai cikakken iko
  • Wasu sun ce akwai ministocin da ya kamata a sallama daga aiki domin babu abin kirkin da suka tabuka a ofishinsu
  • Shugaban kasa Tinubu ya sha alwashin zai rabu da duk ministan tarayya da ya dauko kuma ya gaza tabuka komai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Yayin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke cika shekara guda a ofis, jama’a sun fadi ra’ayinsu game da ministocinsa.

Imran Muhammad wani ffitaccen mai tallata APC a kafafen a kafofin sadarwa, ya nemi jin ra’ayin jama’a a kan ministocin kasar.

Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya ce zai kori wasu Ministoci Hoto: @Modrismalagi
Asali: Twitter

Legit ta duba yadda Malam Imran ya jero ministocin a dandalin X, mutane suka ware na sallama da wadanda suka dace a bari a aiki.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministocin da mutane suke so a kora

An fara ne da irinsu Jamila Ibrahim Bio wanda ita ce ministar matasa, kusan 73% sun ba da shawarar Bola Tinubu ya yi waje da ita.

Akasari sun ce a kori ministoci irinsu Uche Nnaji, Abubakar Momoh, Gboyega Oyetola da Uju Kennedy Ohanenye daga mukamansu.

Da aka zo kan Lola Ade-John, sama da mutane 800 a cikin 945 suka ce a kori ministar yawan bude idon, suna ganin ba ta aikinta.

...Ministocin da ba su da farin jini

Mutane 213 rak cikin kusan 800 suka zabi Ibrahim Gaidam ya cigaba da zama ministan harkokin ‘yan sanda a gwamnati.

Idan jama’an X za a bari da Cif Adebayo Adelabu, ministan makamashin ba zai kwana a kujerarsa ba, 73% sun ce a fatattake shi.

Kara karanta wannan

Shekara 1 a ofis: Jerin ministoci 10 da suka fi kowa kokari a gwamnatin Tinubu

Jama'a sun zabi Balarabe Abbas Lawal ya sauka daga kujerar ministan muhalli duk dai wasu da yawa sun ce yana taka rawar gani.

Ministoci: An yabi Umahi, Wike da Ojo

Da-dama daga cikin masu bibiyar shafin sun yarda Bunmi Ojo ya cancanci mukaminsa, haka abin yake da aka zo kan David Umahi.

Saura kiris jama’a su rabu biyu a kan ministan gona, Abubakar Kyari, wasu na cewa ya cancanci karin lokaci, wasu kuwa sun ce sam.

Kusan duk wanda ya kada kuri’a zai ce Yusuf Tuggar yana aiki, shi ma Ministan harkokin jirage, Festus Keyamo ya samu karbuwa.

Jama’a sun ce Farfesa Tahir Mamman yana kokari a kujerar Ministan ilmi, wannan ne ra’ayin da-dama kan takwarwansa, Nyesom Wike.

Ra'ayin mutane a kan sauran Ministocin Tinubu

Da aka zo ga Bello Matawalle da Muhammad Badaru Abubakar, an yi masu shaidar rashin abin kwarai, haka zalika Cif Dele Alake.

Sauran masu farin jini wajen masu amfani da X su ne: Hannatu Musawa, John Enoh, Ahmad Dangiwa, Lateef Fagbemi, Bosun Tijjani

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki zafi kan ministocinsa, ya fadi wadanda zai kora daga mukamansu

A bangaren Wale Edun, Joseph Utsev, Prince Audu, Sa’idu Alkali da Zephaniah Jisalo, wasu sun ce babu dalilin ajiye su a majalisar FEC.

Karin kudi da Ministan makamashi

A kwanakin baya an kawo rahoto Muhammad Jameel ya bada labarin mutumin da ya sha kudin wutar lantarkin N47m a kwanaki 30.

White Nigerian ya bukaci gwamnatin tarayya ta tsoma baki domin a ceci ‘yan kasuwa a Najeriya bayan an yi karin kudin wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng