Kano: Adadin Wadanda Suka Mutu a Harin Masallaci Ya Karu, Sanata Ya Ba da N15m

Kano: Adadin Wadanda Suka Mutu a Harin Masallaci Ya Karu, Sanata Ya Ba da N15m

  • Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya ba da gudunmawa mai karfi bayan harin da aka a masallaci
  • Sanata ya ba da gudanarwar N15m domin tallafawa wadanda abin ya shafa da siyan makabarta da za a binne mamata a yankin
  • Wannan na zuwa ne yayin da adadin wadanda suka mutu a yanzu ya kai mutane 21 dalilin kona masallaci da wani matashi ya yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Adadin mutanen da suka mutu a harin da wani matashi ya kai cikin masallaci a jihar Kano sai karuwa ya ke yi.

A yanzu haka adadin mutanen da suka mutu a harin masallaci ya kai 21 a karamar hukumar Gezawa.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ake zargin yana kai wa 'yan bindiga makamai a Plateau

Adadin wadanda suka mutu a harin masallaci ya karu yayin da sanata ya ba da gudunmawa
Sanata Barau Jibrin ya ba da N15m game da harin masallacin Kano. Hoto: Barau I Jibrin.
Asali: Facebook

Kano: Yawan wadanda suka mutu a harin

Mazauna yankin suka ce sun binne mutane 21 waɗanda mafi yawansu dattawa ne a harin da aka kai a ranar 15 ga watan Mayu, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya kai ziyarar jaje ga mutanen yankin inda ya tallafa da N15m, cewar Tribune.

Barau ya ce daga cikin N15m din, za a yi amfani da N10m domin siyan filin binne mamata sai kuma N5m ga iyalan wanda suka mutu da kuma wadanda suka ji rauni.

Gudunmawar Barau ga wadanda abin ya shafa

"Na ba da N10m domin siyan filin da za a rika binne mamata da kuma N5m domin iyalan wadanda abin ya shafa."

- Barau Jibrin

Har ila yau, Sanata Barau ya yi alkawarin gina katafaren masallaci na zamani a yankin domin maye gurbin wanda aka rasa dalilin harin.

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun sutu a harin 'bam' da aka kai masallacin Kano

Ganduje ya magantu kan harin masallacin Kano

Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci masu hannu da shuni su taiimakawa iyalan waɗanda harin masallaci ya shafa a jihar Kano.

Ganduje ya roƙi a taimakawa dangin mutanen ne yayin da yake miƙa sakon ta'aziyya ga dangin waɗanda suka rasa rayuwarsu.

Wannan na zuwa ne bayan harin da wani matashi ya kai ana tsaka da sallar asuba a jihar da ya yi ajalin mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel