Sojoji Sun Kai Farmaki Kan ’Yan Ta’adda, Sun Ceto Wasu Jami'an Soji da Aka Sace

Sojoji Sun Kai Farmaki Kan ’Yan Ta’adda, Sun Ceto Wasu Jami'an Soji da Aka Sace

  • Rundunar sojin kasar Najeriya ta sanar da yin nasara kan gungun yan ta'adda daban-daban a yankunan jihar Benue
  • Sojojin sun kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu daga cikin yan bindigar da suka fitini jihar
  • Har ila yau, rundunar sojin ta bayyana irin manyan makamai da sauran abubuwan da ta kama wajen 'yan ta'addan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan yan ta'adda da dama a yankunan jihar Benue.

Sojojin sun kai farmaki ne a kananan hukumomin Ukum da Gwer inda yan bindiga suka yi garkuwa da mutane da dama ciki har da jami'an soji.

Kara karanta wannan

'Yan haramtacciyar kungiyar IPOB sun budewa sojoji wuta, jami'an Najeriya sun mutu

Sojan Ng
Sojoji sun kashe yan ta'adda tare da ceto mutane a Benue. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A jawabin da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Facebook ta nuna cewa sun fafata da yan ta'addan kafin samun nasara a kan su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ceto wadanda aka sace

Bayan kai farmaki maboyar yan bindiga a Sankara da ke karamar hukumar Ukum, sojojin Najeriya sun ceto mutane biyu da aka sace.

Haka zalika rundunar ta ceto jami'an soji biyu da aka sace a karamar hukumar Gwer tare da wasu fasinjoji goma.

Dakarun Sojoji sun kashe yan bindiga

Sojojin da suka fita farautar yan bindigar sun fafata da su kafin daga karshe su hallaka wasu daga cikinsu.

A yayin artabun da suka yi, sojojin sun kashe masu garkuwa da mutane uku a karamar hukumar Ukum.

Jami'an Sojoji sun kwato makamai

Sojojin sun samu kwato bindiga kirar AK47, bindiga kirar gida, wayar hannu, kayan sojoji da babur daya a karamar hukumar Ukum.

Kara karanta wannan

Dubun Baleri ta cika: Sojojin kasar Nijar sun kwamushe ɗan ta'addan da ake nema

A daya bangaren kuma sun kwato radiyo, layukan waya 22, shanu 30, na'ura mai ƙwaƙwalwa wayoyin hannu kirar Samsung da Citel da sauransu.

Sojoji sun kashe yan bindiga a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Nigeriya ta bayyana cewa jami'anta sun kai harin kwantan-bauna kan wasu 'yan ta'adda a Kaduna.

A sakon da rundunar ta wallafa, ta sanar da kwato muhimman kaya irin su bindiga da kayan sufuri daga bata-garin da suka addabi al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel