Sarauta: Bayan Gwamnatin Kano Ta Nemi Afuwa, Abba Ya Gana da Ribadu a Abuja

Sarauta: Bayan Gwamnatin Kano Ta Nemi Afuwa, Abba Ya Gana da Ribadu a Abuja

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya gana da Malam Nuhu Ribadu
  • Gwamna ya yi ganawar da mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro a yau Alhamis 30 ga watan Mayu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gana da mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu a Abuja.

Gwamnan Kano ya yi ganawar da tsakar ranar yau Alhamis 30 ga watan Mayu duk da kokarin zargin Nuhu Ribadu da hannu a rikicin sarautar jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Hakimai na cigaba da yiwa Sanusi II mubaya'a duk da barazanar umarnin Kotu

Abba Kabir ya gana da Nuhu Ribadu yayin da ake dambarwar sarautar Kano
Abba Kabir ya yi wata ganawa ta musamman da Nuhu Ribadu a Abuja. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Kano: Abba ya gana da Nuhu Ribadu

Abba Kabir ya bayyana haka ne a yau Alhamis 30 ga watan Mayu a shafinsa na X inda ya ce sun yi ganawa mai fa'ida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na yi wata ganawa mai fa'ida da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da ranar yau Alhamis a Abuja."

- Abba Kabir

Rikici tsakanin Ribadu da gwamnatin Kano

Duk da ba a sanar da musabbabin wannan ganawa ba amma wasu na ganin yana da nasaba da dambarwar siyasar jihar Kano

Tun farko mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdulsalam Aminu Gwarzo ya zargi Nuhu Ribadu da hannu a rikicin sarautar jihar.

Gwarzo ya ce Ribadu ne ya dauki nauyin jirage guda biyu domin dawo da Aminu Ado Bayero Kano.

Sai dai a bangarensa, mai ba shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro ya musanta wannan zargi da ake yi kansa.

Kara karanta wannan

Duk da umarnin kotu da ke neman sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna ya gana da Sarki

Gwamnatin Kano ta ba Nuhu Ribadu hakuri

Daga bisani, Ribadu ya bukaci Gwarzo ya janye kalamansa ko kuma su hadu a kotu.

Bayan barazanar Ribadu, Gwarzo ya fito ya ba da hakuri inda ya ce sun samu bayanai ne da ba su inganta ba.

Hakimai na mubaya'a ga Sanusi II

A wani labarin, kun ji cewa wasu daga cikin Hakimai da Malaman addini na ci gaba da mubaya'a ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Wannan na zuwa ne duk da umarnin kotu kan rashin ingancin kujerar da Muhammadu Sanusi II ke kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.