Kano: Hakimai Na Cigaba da Yiwa Sanusi II Mubaya'a Duk da Barazanar Umarnin Kotu

Kano: Hakimai Na Cigaba da Yiwa Sanusi II Mubaya'a Duk da Barazanar Umarnin Kotu

  • Bisa ga dukkan alamu zaman lafiya ta fara dawowa Kano bayan dambarwar sarautar jihar na tsawon kwanaki da aka yi
  • Hakimai da shugabannin addinai da-dama sun nuna goyon baya ga sabon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II
  • Wannan na zuwa ne duk da umarnin Babbar kotun jihar kan tuge Sarkin daga fadarsa saboda rashin bin ka'ida yayin mayar da shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaban da dambarwa kan Sarautar Kano, Hakimai na ci gaba da nuna mubaya'a da Muhammadu Sanusi II.

Masu ruwa da tsaki a kungiyar Tijjaniya da wasu malaman addinin Musulunci suna ci gaba da nuna goyon baya ga sabon Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Duk da umarnin kotu da ke neman sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna ya gana da Sarki

Hakimai da sauran jama'a suna nuna goyon bayan ga Sanusi II Kano
Manyan mutane da Hakimai a jihar Kano na ci gaba da mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II. Hoto: @Imranmuhdz.
Asali: Facebook

Kano: Sanusi II na samun goyon baya

Daily Trust ta tattaro cewa manyan mutane kamarsu Khalifa Sayyadi Bashir da Khalifa Abdullahi Uwaisu da Sheikh Ibrahim Shehu Maihula da Barrister Habibu Dan Almajiri sun yi mubaya'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duka sun nuna goyon baya ga sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II duk da umarnin kotu kan rawaninsa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara samun zaman lafiya a jihar yayin da mutane ke ci gaba harkokinsu cikin lumana.

Duk da kasancewar jami'an tsaro a fadar Sarkin da kuma inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ke, mutane sun ci gaba da lamuransu a yankin.

Jama'an jihar Kano da rikicin sarauta

Wani mazaunin yankin Dakata, Alhaji Kabiru Abubakar ya ce mutane yanzu sun fi damuwa da abincin da za su ci fiye da waye zai zama sarki.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauya ya feɗe gaskiya, ya nemowa Aminu Ado da Sanusi II mafita

Kabiru ya ce yana da kwarin guiwar cewa shugabannin addinan da na siyasa za su kawo karshen matsalar cikin ruwan sanyi.

Hajiya Aishatu Danlami ta yabawa Gwamna Abba Kabir da ya hana zanga-zanga inda ta ce hakan ya dakile lalacewar tsaron jihar.

Sanusi II: Kudancin Kano sun bayyana matsayarsu

Kun ji cewa masu ruwa da tsaki a yankin Kudancin Kano sun yi martani kan rikicin sarautar jihar Kano da ke ciki.

Dattawan sun bayyana cewa ya kamata a mayar da sarakunan da aka tube ba bisa ka'ida ba kan kujerunsu na sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel