Mahajjatan Najeriya 20,000 basu da lafiya

Mahajjatan Najeriya 20,000 basu da lafiya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar cikin yawan Mahajjatan Najeriya da suka tafi kasa mai tsarki a wannan shekarar,  guda 20,000 ke karban magani a dakunan shan magani dake birnin Madinah da garin Makkah, kasar Saudiya.

Mahajjatan Najeriya 20,000 basu da lafiya
Wasu mahajjatan Najeriya a hanyar su ta zuwa saudi

Hukumar kula da mahajjata ta kasa wato National Hajj Commission (NHC), ce ta sanar da hakan, cewa ta kula da mahajjatar ta hanyar tawagar likitar kasa.

Da yake Magana kan ci gaban, shugaban tawagar liktan mahajjata, Dakta Ibrahim Kana, yace yawan marasa lafiya na wannan shekarar ta karu idan aka kwatanta da yawan mutanen da sukayi jinya a shekarar bara.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar masu digiri 100,000 aiki

A cewar sa, marasa lafiya 5000 aka yi wa magani sakamakon sake fasalin da aka gabatar daga shugaban hukumar tare da harhada dukkan tawagar Likitoci a guri daya.

Aikin hajjin shekarar nan ta 2016 ya samu wasu kalubale wanda ya hada rahoto daga hukumar kula da safaran miyagun kwayoyi wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) cewa anyi wa wata mata da zata tafi birnin Madina, kasar Saudiya domin ta yi aikin hajji, gwajin miyagun gwayoyi wanda sakamako ya nuna cewa tana dauke da hodar Iblis, a ranar Juma’a 2 ga watan Satumba, a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel