Guzirin Sigari Ko Goro: NAHCON Ta Gargadi Alhazan Najeriya Masu Shirin Tafiya Saudiya

Guzirin Sigari Ko Goro: NAHCON Ta Gargadi Alhazan Najeriya Masu Shirin Tafiya Saudiya

  • An gargadi maniyyata daga Najeriya da su guji yin safarar haramtattun kayayyaki, irinsu kwayoyi, sigari da goro zuwa Saudiya
  • Hukumar alhazai ta Najeriya ta yi wannan gargadin inda ta ce kasar Saudiyya na da tsauraran dokoki kan safarar miyagun kwayoyi
  • NAHCON ta yi kira ga alhazan da suyi amfani da wannan damar ta musamman domin yin bautar Allah madaukin Sarki ka'in da na'in

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta gargadi maniyyata aikin hajjin 2024 da su guji safarar haramtattun kayayyaki zuwa Saudiya.

Haramtattun kayayyakin sun hada da miyagun kwayoyi, goro, sigari da sauran abubuwan da kasar ta hana a shigar mata da su.

Kara karanta wannan

Hajji: Hukumomi a Saudiyya za su koro mahajjata, NAHCON ta gargadi ƴan Najeriya

NAHCON ta gargadi alhazan Najeriya
NAHCON ta gargadi alhazan Najeriya kan tafiya Saudiya da haramtattun kaya. Hoto: @MoHU_En
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito NAHCON ta ce Saudiyya na da tsauraran dokoki kan fataucin miyagun kwayoyi yayin da hukuncin kisa ke jiran masu karya dokokin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saudiya na da tsauraran dokoki" - NAHCON

NAHCON ta yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar hulda da jama’a Fatima Sanda Usara a ranar Alhamis a Abuja.

Fatima Sanda ta ce:

“An gargadi maniyyata aikin hajjin 2024 da su guji tafiya da haramtattun kayayyaki irinsu kwayoyi, goro, tabar sigari da sauransu, zuwa kasar Saudiyya.
“Ana tunatar da mahajjata cewa a matsayinta na kasar da ta kafu a kan addini da al’adu, Saudiyya na yanke hukuncin kisa ga masu fataucin miyagun kwayoyi.

NAHCON ta gargadi alhazan Najeriya

Ko a taron da hukumar ta gudanar na fara jigilar maniyyata a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi ya yi irin wannan gargadin.

Kara karanta wannan

'Abin kunya': NBA ta soki Lauyoyi da Masu shari'a kan dambarwar masarautar Kano

Jaridar Vanguard ta ruwaito Arabi ya yi kira ga alhazai da su yi amfani da wannan damar ta musamman na yin bautar Allah ka'in da na'in tare da gujewa ayyukan da aka haramta.

"Mutum ya kuka da kansa idan har aka kama shi da laifin kin bin dokokin da aka gindaya a aikin Hajji a Saudiya domin ba wanda zai hana doka tayi aiki a kansa."

- Jalal Arabi.

Filato: Maniyyata 135 ba za su je Hajji ba

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla maniyyata 135 daga jihar Filato ne ba za su samu damar sauke farali a aikin Hajji na wannan shekarar ba.

Maniyyatan sun rasa damar zuwa sauke faralin ne sakamakon karin kudin aikin hajjin bana da aka yi, kuma duk da cewa sun biya karin kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel