Luguden Wutan Sojojin Sama Ya Soye 'Yan Ta'adda a Jihohin Katsina da Borno
- Rundunar sojojin saman Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 30 a jihohin Borno da Katsina
- Dakarun rundunar da ke aiki a Operation Hadarin Daji da Operation Hadin Kai ne suka kai hare-haren kan maɓoyar ƴann ta'addan cikin daji
- Daraktan hulɗa jama'a da yaɗa labarai na rundunar, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarunta sun hallaka ƴan ta'adda 30 a hare-haren da suka kai a jihohin Katsina da Borno.
Rundunar ta ce sojojinta na Operation Hadarin Daji da Operation Hadin Kai ne suka kai hare-haren a maɓoyar ƴan ta'addan a wasu jihohi.
Daraktan hulda da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojojin sama suka sheƙe ƴan ta'adda
Edward ya ce harin da dakarun rundunar na Operation Hadarin Daji suka kai a yankin Arewa maso Yamma a ranar 27 ga watan Mayu, ya yi nasarar kawar da wasu ƴan ta’adda da ke biyayya ga shugaban ƴan ta'adda da aka fi sani da Babura.
Ya ce an kai hare-haren ne a kusa da ƙauyukan Bakai, Bakarya, da kuma maɓoyar ƴan ta'adda a ƙauyen Ƴartsintsiya a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
Dakarun sooji sun kashe 'yan ta'adda
A cewarsa bayanan da aka samu bayan harin sun nuna cewa an kashe ƴan ta’adda kusan 30, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Ya ce an kuma tabbatar da cewa Babura da kyar ya tsira da ransa, yayin da aka kashe akasarin mayaƙansa.
Gabkwet ya ce, an kuma kai hare-hare makamancin wannan ta sama a wannan rana a maɓoyar ƴan ta'adda da ke Tumbun Fulani kusa da tafkin Chadi.
Sojoji sun fatattaki ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta yi nasarar hallaka ƴan ta'adda tare da lalata maɓoyarsu a jihar Neja.
An kai harin ne a maboyar ƴan ta’addan da ke ƙaramar hukumar Shiroro, a sansanin shugaban ƴan ta’adda, Malam Umar da wasu kwamandoji a dajin Allawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng