Gwamnatin Tinubu Ta Dawo da Shirin Rage Talauci ga 'Yan Najeriya Miliyan 75

Gwamnatin Tinubu Ta Dawo da Shirin Rage Talauci ga 'Yan Najeriya Miliyan 75

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da shirin ba da tallafin kuɗi na kai tsaye ga ƴan Najeriya miliyan 75 a gidaje miliyan 50
  • Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya tabbatar da dawo da shirin domin rage raɗaɗi ga talakawan Najeriya masu fama da talauci
  • A baya dai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ne bayan zarge-zargen da ake yi kan yadda ake gudanar da shirin tallafin kuɗin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta dawo da shirin ba da tallafin kuɗi ga ƴan Najeriya.

Gwamnatin ta ce shirin zai riƙa biyan kuɗi kai tsaye ga ƴan Najeriya miliyan 75 da ke cikin gidaje miliyan 50 domin rage raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki, musamman talakawa.

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun fara kai hari da manyan bindigu," Gwamna Raɗda ya tura saƙo ga Tinubu

Gwamnati za ta ci gaba da ba 'yan Najeriya tallafin kudi
'Yan Najeriya miliyan 75 za su amfana da shirin ba da tallafin kudin Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

An yiwa shirin tallafin kudi garambawul

Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa an yi gyaran fuska ga shirin ba da tallafin kuɗin na kai tsaye domin magance zamba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya sanar da hakan a wajen taron bayanin ministocin domin cikar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu shekara ɗaya a kan mulki a ranar Talata a Abuja.

Ministan ya kuma bayyana cewa tattalin arziƙin ƙasar nan yana ƙara haɓaka, rahoton da jaridar The Nation ta tabbatar.

A baya dai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin bayan zargen-zargen da aka yi kan aikata rashin gaskiya a wajen gudanar da shirin.

Meyasa gwamnatin Tinubu ta dawo da shirin?

Da yake yin ƙarin haske kan dawo da shirin, ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar dawo da shirin domin ragewa talakawan Najeriya raɗaɗi.

Kara karanta wannan

"Mun shirya tsaf," 'Yan sanda sun ƙara ɗaukar mataki kan rigimar sarautar Kano

"Gwamnati ta sake dawo da shirin ba da tallafin kuɗi wanda zai riƙa biyan ƴan Najeriya miliyan 75 kuɗi kai tsaye a gidaje miliyan 50."
"An ƙara inganta hanyoyin samun lamuni, inda aka ware Naira biliyan ɗaya (N1bn) domin ba da lamuni, sannan an ba da tallafin N50,000 ga ƙananan masana'antu miliyan ɗaya."

- Wale Edun

Murnar cikar Tinubu shekara 1 a mulki

A baya rahoto ya zo cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin da zai ɗauki alhakin gudanar da taron bikin cika shekara ɗaya na mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Taron da za a gudanar domin tunawa da ranar 29 ga watan Mayu, 2023, zai waiwayi nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu a cikin shekara ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng