An Karbi Masoyi Mai Tattaki Tun Daga Gombe Domin Ganin Sheikh Isa Pantami

An Karbi Masoyi Mai Tattaki Tun Daga Gombe Domin Ganin Sheikh Isa Pantami

  • Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya tabbatar da karbar wani dan jihar Gombe da ya fara tattaki domin zuwa wajensa a Abuja
  • Alhaji Mustapha Isawa ya karbi mai tattakin a yau Talata a madadin Sheikh Pantami a gidansa da ke jihar Bauchi
  • Tun a jiya da Sheikh Pantami ya samu labarin mai tattakin ya isa garin Alkaleri a jihar Bauchi ya sanar da cewa ya dakata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

jihar Bauchi - Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya sanar da karbar wani mutum mai suna Auwal da ya fara tattaki domin zuwa wajensa.

Mai tattaki
An karbi mai tattaki domin ganawa da Sheikh Pantami a Bauchi. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Malam Auwal ya fara tattaki ne daga jihar Gombe zuwa Abuja domin ganawa da Sheikh Pantami kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tsaya daga can: Pantami ya dakatar da matashin da ke tattaki zuwa wajensa a Abuja

A yau Talata, wakilin Sheikh Pantami, Alhaji Mustapha Isawa ya karbi mai tattakin a gidan Sheikh Pantami da ke Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai tattakin Pantami ya isa Bauchi lafiya

A cikin bayanan da Sheikh Pantami ya wallafa ya nuna cewa mai tattakin ya isa jihar Bauchi cikin aminci.

Ya kuma tabbatar da cewa wanda ya karbe shi a madadinsa ya yi godiya ga mai tattakin tare da masa fatan alheri.

Ga abin da yake cewa:

"Alhamdu lil Laah. A yau wakilin Farfesa Pantami, Alhaji Mustapha Isawa (wanda shi ne Wamban Isawa) ya karbi Malam Auwal Gombe a Bauchi a cikin aminci.
"An yiwa Malam Auwal godiya matuka da gaske da kuma fatan alheri."

-Sheikh Isa Ali Pantami

Yaushe mai tattakin zai dawo Gombe?

Kamar yadda malamin ya ba da umurnin dawo da mai tattakin Gombe, ya sanar da cewa da zarar ya huta za a maido shi gida.

Kara karanta wannan

Shahararren malamin Kano ya yi magana bayan an tashi da sarakuna 2 a gari

Sheikh Pantami ya kuma yiwa wannan tafiya addu'a da fatan alheri bisa soyayya da ya nuna masa.

Isa Pantami ya yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Isa Pantami ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka yi watsi da tsarin dakile matsalar tsaro a kasar nan.

Pantami ya ce a lokacin da ya ke Minista ya kawo tsarin hada lambobin NIN da layukan mutane domin magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng