Tsaya Daga Can: Pantami Ya Dakatar da Matashin da ke Tattaki Zuwa Wajensa a Abuja

Tsaya Daga Can: Pantami Ya Dakatar da Matashin da ke Tattaki Zuwa Wajensa a Abuja

  • Matasa a Najeriya sun dade suna wata al'adar tattaki domin ganawa da yan siyasa ko shahararrun mutane a wurare masu nisa
  • A jiya Litinin wani matashi mai suna Auwal ya dauki hanya daga Gombe yana tattaki a kan keke domin ganawa da Isa Ali Pantami
  • Biyo bayan ganin labarin, Sheikh Pantami ya yi umurni da dakatar da matashin tare da bayyana yadda za a mayar da shi gida

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Wani matashi mai suna Auwal ya dauki damarar tattaki bisa keke daga Gombe zuwa Abuja domin ganawa da sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.

Pantami
Sheikh Pantami ya dakatar da mai tattaki domin kare lafiyarsa. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Sheikh Isa Ali Pantami Pantami ya bayar da umurnin dakatar da matashin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Rahotanni sun tabbatar da cewa matshin yana karamar hukumar Alkaleri ne labarin ya riski Sheikh Pantami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isa Pantami ya dakatar da mai tattaki

Bayan an sanar da Sheikh Pantami cewa wani matashi mai suna Auwal yana kan hanya zuwa wajensa daga Gombe, ya bada umurnin ya tsaya daga Bauchi.

Ya ce ya tsaya a karbe shi a gidansa da yake Bauchi daga nan sai a saka shi a mota da shi da keken da yake tattaki da shi zuwa gida Gombe.

Ga abin da yace:

"Sai a saka shi a mota tare da kekensa zuwa Gombe. Muna godiya sosai, Allah ya biya shi da Aljannah."

-Sheikh Isa Ali Pantami

Pantami: Dalilin dakatar da mai tattaki

A cikin sakon da malamin ya wallafa ya bayyana cewa tabbatar da lafiyar matashin abu ne mai muhimmanci a wajensa.

Kara karanta wannan

Shahararren malamin Kano ya yi magana bayan an tashi da sarakuna 2 a gari

Saboda haka Sheikh Pantami ya dakatar da matashin ne domin kare lafiyarsa da kuma rayuwarsa daga hatsarin da zai iya fuskanta a hanyar tattakin.

Duk da haka malamin ya yi umurni da a karrama mai tattakin a madadinsa idan ya iso gidansa dake jihar Bauchi.

Dakta Yakubu Sani Wudil ne ya sanar da Sheikh Pantami a kan tattakin da matashin ya fara zuwa wajensa.

Pantami ya aika sakon ta'aziya

A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin dattawan jihar Gombe kuma marubuci, Gidado Bello Akko ya rasu a Zariya kuma Farfesa Said Yunus ne ya jagoranci yi masa sallah.

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya shiga cikin jerin fitattun mutane da suka nuna alhini kan rasuwar babban marabucin tare da aika sakon jaje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel