“Yan Bindiga Sun Ki Fita Daga Kauyenmu Kwanaki Bayan Sun Kai Mummunan Hari”

“Yan Bindiga Sun Ki Fita Daga Kauyenmu Kwanaki Bayan Sun Kai Mummunan Hari”

  • Manoma a jihar Niger sun koka kan yadda yan bindiga suka cigaba da mamaye garinsu bayan sun kai musu mummunan hari
  • Rahotanni sun nuna cewa yan bindiga sama da 300 ne suka shiga garin suna aikata ayyukan ta'addanci kan fararen hula
  • Wasu mazauna garin dai yanzu haka sun yi hijira zuwa wasu ƙauyukan yayin da wasu kuma suna hannun yan bindigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Yan bindiga da suka kai hari garin Kuchi da ke karamar hukumar Muya a Jihar Neja sun ki barin garin.

Bago of Niger
Yan bindiga sun kori mutane a kauyen jihar Neja. Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen garin na kokawa kan yadda al'amura suka tsaya cak saboda yan bindigar.

Kara karanta wannan

Ranar yara: Tinubu ya yi alkawura kan inganta rayuwar kananan yara

A satin da ya wuce ne gungun yan bindiga suka kai hari garin tare da kashe mutane da dama da kama wasu bayin Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me 'yan bindigar su ke yi a Kuchi?

Wani mutumin garin da ya gudu zuwa yankin Sarkin Pawa ya bayyanawa yan jarida cewa yan bindigar suna ayyukan ta'addanci ne a garin yanzu haka.

Ya ce sun cigaba da satar shanun mutanen garin da sauran kayayyakinsu saboda haka suke buƙatar taimakon gaggawa.

Shugaban ƙaramar hukuma ya yi bayani

Shugaban ƙaramar hukuma Munya, Aminu Najume ya yi karin haske kan lamarin a wata hira da ya yi da yan jarida.

Ya ce yan bindiga da dama suka shiga garin suna harbe harbe. A cewar shugaban, ayyukan su ya yi kama da na Boko Haram da ISWAP.

Mutanen da yan bindiga suka kashe

Kara karanta wannan

Filato: Adadin mutanen Zurak da suka mutu a harin 'yan bindiga ya karu

Tun a karon farko da suka kai harin ranar Jumu'a, yan bindigar sun kashe yan banga shida da fararen hula hudu.

Wani mazaunin garin ya shaida cewa sama da mutane 160 yan bindigar suka yi garkuwa da su yayin harin da suka kai.

Gwamna ya sake fursunoni a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Muhammad Bago na jihar Neja ya ceci Fursunoni 80 daga gidajen gyaran hali daban-daban a fadin jihar.

Bago, ya roƙi waɗanda suka shaƙi iskar 'yanci su yi amfani da wannan damar wajen aikata ayyuka nagari maimakon laifin da ka iya dawo da su gidan yari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel