'Yan Kwadago Sun Sake Fatali da Sabon Mafi Karancin Albashi, Sun Fadi Abin da Za a Biya

'Yan Kwadago Sun Sake Fatali da Sabon Mafi Karancin Albashi, Sun Fadi Abin da Za a Biya

  • 'Yan kwadago sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashi na N60,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar wanda za a riƙa biyan ma'aikata
  • Ƙungiyoyin na NLC da TUC sun kuma ƙara rage buƙatarsu ta a biya N497,000 zuwa N494, a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi
  • A yanzu dai saura kwanaki uku wa'adin da ƙungiyoyin suka ba gwamnati ya cika kan tattaunawa dangane da batun mafi ƙarancin albashin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta sake yin watsi da sabon mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya ta gabatar.

A wannan karon, ƙungiyoyin ƙwadago da suka haɗa da NLC da TUC sun yi watsi da tayin gwamnatin tarayya na biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

'Yan kwadago sun yi fatali da sabon mafi karancin albashi
Kungiyoyin kwadago sun yi watsi da N60,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigerian Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Albashi: Ƴan ƙwadago sun rage buri

A halin da ake ciki, ƙungiyar ƙwadago ta kuma sauya matsayinta daga N497,000 a makon da ya gabata zuwa N494,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mamba a kwamitin tattaunawa kan batun ƙarin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Najeriya ya bayyana hakan ga wakilan tashar Channels tv.

Ya bayyana cewa wakilan gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu a taron, sun gabatar da mafi ƙarancin albashi na N60,000 a duk wata saɓanin N57,000 da suka gabatar a makon da ya gabata.

Tun da farko dai gwamnati ta gabatar da N48,000 da kuma N54,000 a makon da ya gabata a matsayin mafi ƙarancin albashi, yayin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da su.

Nawa ƴan ƙwadago suke so a biya?

Ƙungiyar kwadago ta kuma gabatar da N615,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi amma daga baya ta janye buƙatar zuwa N497,000 a makon jiya sannan zuwa N494,000 a ranar Talata (yau).

Kara karanta wannan

Gwamna ya cika alkawari ya fara biyan sabon mafi karancin albashi a jiharsa

Har yanzu dai kwamitin tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan bai cimma matsayar kudin da za a riƙa biyan ma’aikatan ba.

Yanzu dai saura kusan kwanaki uku wa’adin ranar 31 ga watan Mayu da ƙungiyoyin kwadago suka ba gwamnati domin kammala tattaunawar ya cika.

NLC ta ja kunnen gwamnoni kan albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun yi gargaɗi ga gwamnonin jihohin da har yanzu ba su fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 ba.

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta ƴan kasuwa ta TUC sun gargaɗi gwamnonin jihohin da su tabbata sun fara biyan N30,000 a ƙarshen watan Mayu ko su ɗauki mataki na gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng