Zargin Satar Kudi: Gwamnatin Kano Ta Dauki Mataki Kan Shugaban ARTV, Mustapha Indabawa

Zargin Satar Kudi: Gwamnatin Kano Ta Dauki Mataki Kan Shugaban ARTV, Mustapha Indabawa

  • Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugaban gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV), Mustapha Indabawa
  • An ruwaito cewa ana zargin Mustapha Indabawa da hada baki da wani Ibrahim M. Bello wajen karkatar da kudi
  • Gwamnan Kano, Alhaji Abba Yusuf ya amince da nadin Hajiya Hauwa Ibrahim a matsayin shugabar ARTV

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Hajiya Hauwa Ibrahim a matsayin mukaddashiyar shugabar gidan talabijin na Abubakar Rimi.

Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan Mustapha Indabawa, shugaban ARTV
Kano: Gwamna Abba ya nada sabuwar shugabar gidan talabijin na ARTV. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

ARTV ta yi sabuwar shugaba a Kano

Nadin na Hajiya Hauwa ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa tsohon shugaban gidan talabijin din, Mustapha Indabawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dakatar da muhimmin aikin da Buhari ya fara a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wasikar nadin mai kwanan wata 27 ga Mayu 2024 na dauke ne da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi.

Wasikar ta umurci Hajiya Hauwa Ibrahim da ta karbi ragamar gudanar da al’amuran gidan talabijin din nan take.

Ana zargin Indabawa da satar kudi

Kafin wannan nadin, Hajiya Hauwa Ibrahim ta kasance mataimakiyar shugaban gidan Talabijin din ne.

Gwamnatin Kano dai ta shigar da tuhume-tuhume guda bakwai da suka shafi hada baki, karkatar da kudi da kashe kudi ba bisa ka'ida ba kan Indabawa da wani Ibrahim M. Bello.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar ta binciki lamarin ne biyo bayan wani koke da aka rubutawa gwamnan jihar kan Indabawa da Bello, a cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

Dahiru Bauchi ya aika sako zuwa Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya aika muhimmin sako ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi Gwamna Yusuf da ya mutunta umarnin babbar kotun tarayya da ta dakatar da shi daga rusa masarautun jihar Kano da kuma nada sabon sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel