Bankin CBN Ya Kori Manyan Mutane 7 Daga Aiki, Zai Tsige Ƙarin Daraktoci Sama da 10

Bankin CBN Ya Kori Manyan Mutane 7 Daga Aiki, Zai Tsige Ƙarin Daraktoci Sama da 10

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya fara shirin korar daraktoci 19 daga aiki bayan matakin da ya ɗauka ranar Jumu'a da ta gabata
  • Rahoto ya nuna CBN ya kori daraktoci bakwai a makon jiya, biyar daga cikin sun lashi takobin neman adalci a gaban kotu
  • Daraktoci 12 da har yanzun ba a tura masu takardun kora ba suna da masaniyar abin da ke shirin faruwa nan da ƴan kwanaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun nuna cewa daraktoci 19 a babban bankin Najeriya na shirin rasa aikinsu nan da ƴan kwanaki a wani garambawul da bankin ya fara.

Jaridar The Nation ta ce CBN na shirin korar waɗannan manyan ma'aikata daga aiki biyo bayan sallamar daraktoci bakwai da babban bankin ya yi ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi malamin Musulunci 1 da suke goyon bayan ya tattauna da ƴan bindiga

CBN na shirin korar daraktoci 19.
CBN ya fara tankade da rairaya a tsakanin daraktoci Hoto: CBN
Asali: Facebook

Bankin CBN ya kori daraktoci 7

Yayin da biyu daga cikin daraktocin da aka kora suka ɗauki ƙaddara, sauran 5 kuma na shirin daukar matakin shari’a kan abin da suka dauka a matsayin korarsu ba bisa ka’ida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktocin da suka rungumi kaddara suna fuskantar tuhuma a hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) saboda rawar da suka taka a rahoton binciken Obaze.

Sauran daraktoci biyar da babban bankin ya raba da aikinsu sun nuna fushi ne saboda babu wani tabon rashin gaskiya, haka kurum aka sallame.su.

Wata majiya a CBN ta nuna danuwa kan yadda aka kori daraktoci ba tare da ba su wani ladan aiki ba, musamman idan aka yi la'akari da tsawon lokacin da suka shafe suna aiki.

Haka nan kuma majiyar ta ce babu wata tuhumar almundahana a kansu, amma duk da haka an sallame su ba tare da wani kunshi kuɗi ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Ana shirin ƙara sallamar wasu Darektocin CBN

An tattaro cewa ragowar daraktoci 12 da har yanzu ba a tura masu takaradar kora ba sun san ana dab da sallamarsu daga aiki.

Wasu ma’aikata sun yi kira ga CBN a madadin daraktocin da abin ya shafa cewa a sake duba korar da aka yi musu, a mayar da ita ritaya domin su samu alawus alawus din su.

Abin da ke faruwa a CBN ya haddasa kace-nace tsakanin ma'aikata da tasirin da korar daraktocin ka iya yi ga aikin babban bankin, cewar rahoton Daily Trust.

Tinubu ya gana da shugabannin APC a Villa

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da jagororin jam'iyyar APC reshen jihar Edo a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Bayanai sun nuna cewa zaman zai maida hankali wajen warware dukkan wani rikicin cikin gida da APC ta shiga bayan zaɓen fidda gwani a Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel