An Dauki Mataki Kan 'Dan Sandan da Aka Nadi Bidiyonsa Yana Karbar ‘Na Goro’ a Imo

An Dauki Mataki Kan 'Dan Sandan da Aka Nadi Bidiyonsa Yana Karbar ‘Na Goro’ a Imo

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta hukunta wani jami’inta mai suna Sifeta Isong Osudueh da aka nadi bidiyonsa yana karbar na goro
  • Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya ce an ragewa Sifeta Isong matsayi saboda ladabtarwa
  • Alhaji Mamuda Tukur, a zantawarsa da Legit Hausa ya roki gwamnatin tarayya da ta kara albashi da alawus ga 'yan sandan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta ce ta dauki mataki kan jami’anta mai suna Sifeta Isong Osudueh da aka nadi bidiyonsa yana karbar cin hanci.

Rundunar ta ce ta rage wa Sifeta Isong matsayi saboda karbar 'na goro' hannu masu ababen hawa a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

An dauki mataki kan dan sandan da aka kama yana karbar cin hanci a Imo
Rundunar 'yan sandan Imo ta hukunta jami'inta da aka kama yana karbar cin hanci. Hoto: @chekwube_henry
Asali: Twitter

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rage wa dan sanda matsayi

Bidiyon da ya bazu a ranar Litinin, ya nuna jami’in yana karbar kudi daga hannun direbobin da ke wucewa ta titin yayin da yake gudanar da bincike.

Ana kuma iya ganin shi yana mika canji ga wasu direbobin a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A cewar sanarwar, an ragewa Osudueh, wanda ke aiki a sashen yaki da ta’addanci a Owerri matsayi bayan ya fuskanci hukuncin ladabtarwa.

Bidiyon dan sanda yana karbar na goro

A lokaci guda kuma, an ba jami'in da ke sa ido kan dan sandan takardar tuhuma saboda rashin kulawa da da'ar jami'an da ke karkashinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sa tukuicin N25m ga duk wanda ya taimaka aka kama waɗanda suka kashe sojoji

Wani mutum mai suna @ChuksEricE ne ya wallafa bidiyon dan sandan yana karbar 'na goro' a shafinsa na X.

Kalli bidiyon a kasa:

"Wannan mataki ya yi dai dai" - Alhaji Tukur

A zantawar Legit Hausa da mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Alhaji Badamasi Tukur, ya ce wannan mataki da aka dauka kan dan sandan ya yi dai dai.

Alhaji Tukur ya ce 'yan sanda masu karbar cin hanci a kan tituna su ne ke jawo ana safarar makamai kasancewar ba sa duba motocin da suka karbi cin hanci a wajen su.

Ya ce idan har 'yan sandan suka ga ana hukunta su haka, dole su daina karbar rashawa wanda zai sa suyi aikinsu yadda ya kamata, abin da zai sa a rika kama masu laifi kenan.

A hannu daya kuma, mai fashin bakin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi karin albashi da alawus ga 'yan sandan domin karfafa masu guiwa da cire masu sha'awar karɓar cin hanci.

Kara karanta wannan

"Karancin kudi": Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki a jami'ar Kano, ta bayyana dalili

Masarautar Kano: Kotu ta ba 'yan sanda umarni

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Kano ta ba 'yan sanda umarnin fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nassarawa.

Haka zalika, kotun ta dakatar da tsofaffin sarakunan Kano biyar daga bayyana kansu a matsayin sarakuna biyo bayan karar da gwamnatin jihar ta shigar a kotun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.