Cin hanci: Bidiyon dan sanda na ba mai abun hawa canjin N900 bayan karbar N1000

Cin hanci: Bidiyon dan sanda na ba mai abun hawa canjin N900 bayan karbar N1000

- Bidiyon wani dan sanda mai karbar cin hanci tare da ba mai abun hawa canji a kan titi ya jawo cece-kuce

- Mai motar ya ba dan sandan dubu daya ne amma sai da dan sandan ya fasa don bashi canji

- Kamar dai wani kasuwanci, an ga dan sandan na neman canji a cikin kudinsa inda ya ba mai abun hawan N900

Cin hanci da rashawa a Najeriya ba sabon abu bane. A halin yanzu ya zama jiki kuma ana ganinsa ba a bakin komai ba ballantana ga masu aikatawa.

Manyan masu taka rawar gani a fannin cin hanci da rashawa a najeriya sune ‘yan sandan Najeriya. Sannanen abu ne idan aka ce suna tare jama’a masu ababen hawa a kan titiuna don karbar na shan ruwa kamar yadda suke cewa.

Wasan buyan da ke tsakanin direbobi da ‘yan sandan yanzu ya zama ruwan dare kuma hatta matukan ababen hawan sun saba da shi. Su kan kirga komai ne tare da kudin da zasu iya kashewa a kan titunan kasar nan. A halin yanzu abun ya zama tamkar harajin kan tituna wanda dole ne biyansa.

Tirkashi: Dan sanda na ba mai abun hawa canjin N900 bayan karbar N1000 (Bidiyo)
Tirkashi: Dan sanda na ba mai abun hawa canjin N900 bayan karbar N1000 (Bidiyo)
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje

Wani bidiyo mai tarin abun mamaki ya karade kafafen sada zumuntar zamani. A bidiyon kuwa, wani dan sandan Najeriya ne ya bayyana yana bukatar cin hanci daga hannun wani direba amma abun sai ya koma tamkar kasuwanci.

A bidiyon da wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita ya wallafa, an ga mai abun hawan na mika kudi ga wani dan sandan kan hanya kamar dai yadda aka saba.

Bayan gaishe-gaishe sai ya mika naira dubu daya ga dan sandan wanda ya fara lalubar aljihunsa don samun canji. Daga baya kuwa sai ga canjin dari tara ya bayyana daga hannun dan sandan bayan ya amshe dubu dayar direban.

Direban mai tafiya daga Legas zuwa Ife ya saba da wannan lamarin na ‘yan sandan kan hanya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel