‘Yan Sanda Sun Damke Manyan ‘Yan Ta’adda 4 da Aka Dade Ana Nema, An Samo Makamai

‘Yan Sanda Sun Damke Manyan ‘Yan Ta’adda 4 da Aka Dade Ana Nema, An Samo Makamai

  • Rundunar 'yan sandan jihar Enugu tayi nasarar cafke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan ta'adda ne a samame daban-daban a fadin jihar
  • Ana zargin hudun ne da dabbbaka ayyukan ta'addanci bayan an kamasu da haramtattun abubuwan ta'addanci
  • A shirye rundunar take da ta gurfanar da wadanda ake zargin da zarar an kammala bincike don yanke musu hukunci daidai da abun da suka aikata

Enugu - Rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta cafke wasu gawurtattun 'yan ta'adda hudu a cikin mako daya yayin da suka kai samame. Suna kokarin ganin sun gurfanar da hatsabiban gaban kotu.

‘Yan sanda
‘Yan Sanda Sun Damke Manyan ‘Yan Ta’adda 4 da Aka Dade Ana Nema, An Samo Makamai. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

A cikin wannan lokacin ne jami'an suka gano bindiga kirar AK47 guda daya da harsasai masu linzami 51 masu tsawon 7.62mm, bindugu kirar hannu uku, bindiga mai jigida daya, abun hada bindigar hannu, carbin harsasai guda 31 da sauran haramtattun abubuwan ta'addanci, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

Kakakin 'yan sandan , DSP Daniel Ndukwe, ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a Enugu yadda ake tunanin wadanda ake zargin suna daga cikin hatsabiban da ke jefa tsoro ga mazauna yankin, inda aka yi nasarar cafkesu tsakanin 1 ga watan Disamba zuwa 6 ga watan.

Ndukwe ya labarta nasarar tazo duba da irin matakan da kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Ammanu ya sanya don yaki da ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ya kara da cewa, yayin amfani da bayanan sirri, jami'an tsaron dake tawagar yaki da kungiyar asiri sun yi nasarar damko Ifeanyi Ngene, mai shekaru 36 a Akwuke cikin lardin Awkunanaw na jihar Enugu, a ranar 6 ga watan Disamba da misalin karfe 9:00 na safe.

Kakakin ya bayyana yadda aka kama Ngene da laifin mallakar haramtattun abubuwa wadanda suka hada da, bindiga kirar AK47 guda daya tare da harsasai masu linzami 51 masu tsawon 7.62mm, abun hada bindiga guda daya da harsasai bindiga 25 da bindiga kirar AK47.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Halaka Abu Na-Iraqi da Abu-Na Masari, Gawurtattun 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Katsina

Ya cigaba da bayyana yadda aka kama Ngene da kayan babban jami'in 'dan sanda, bakaken belt 3 na soji, kayan masu tsaron daji guda biyu, da takalmin soji guda biyu.

A cewar:

"Har ila yau, jami'an dake aiki a ofishin 'yan sandan cikin gari sun cafke Kenechi Ngwuenwo mai shekaru 25 a ranar 6 ga watan Disamba misalin karfe 4:40 yayin gudanar da aikinsu na duba masu bin titin Enugu zuwa Onitsha wajen sabuwar kasuwar Enugu.
"An kama matashin da bindiga kirar hannu da carbin harsasai shida.
"A wani lokaci mai kama da haka, jami'an 'yan sandan dake aiki a Policie Mobile Force-3, yayin sintiri wajen kwanar Ozalla 4 na titin Udi a 1 ga watan Disamba misalin 11:25, sun yi ram gami da kama Amaechi Precious, mai shekaru 25 da wata mota kirar Toyota Sienna tasi wacce ta taso daga Abakaliki, babban birnin Ebonyi zuwa babban birnin Anambra, Awka.”

Ndukwe ya bayyana yadda ake shirin gurfanar da wadanda ake zargin gami da yanke masu hukunci da zarar an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel