Kano: An Shiga Ɗimuwa Bayan Jin Harbe Harbe a Fadar da Aminu Ado Bayero Yake

Kano: An Shiga Ɗimuwa Bayan Jin Harbe Harbe a Fadar da Aminu Ado Bayero Yake

  • A daren jiya Litinin an yi ta jin harbe-harbe da suka tayar da hankulan jama'a daga fadar Nasarawa da ke jihar Kano
  • A fadar Nasarawa, Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ya ke da zama a yanzu haka bayan tube shi da aka yi a makon jiya
  • Wasu mazauna yankin na fargabar ko ana yi harbe-harben ne domin dakile kokarin cafke Aminu Ado bayan umarnin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An shiga fargaba bayan jin harbe-harbe da daren jiya Litinin 27 ga watan Mayu kusa da fadar Nasarawa inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ke.

Fadar tana da nisan mita 300 daga gidan gwamnatin jihar wanda aka hana zirga-zirgan ababan hawa zuwa gefen hanya daya.

Kara karanta wannan

Bidiyon jami'an tsaro sun tare a fadar Nasarawa duk da umarnin kotu kan Aminu Ado

An jiyo harbe-harbe daga fadar da Aminu Ado ya ke
Mutane sun shiga fargaba bayan jiyo harbe-harbe daga fadar Nasarawa da Aminu Ado Bayero yake. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Masaraurar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Jami'an tsaro na sintiri fadar Nasarawa

An jibge jami'an tsaro a fadar da ke cike da mutane da cunkoso kafin barkewar wannan rigima ta sarauta a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mazauna yankin sun zargi harbin da cewa yunkuri ne na dakile kokarin cafke Aminu Ado bayan umarnin babbar kotun jiha.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa Premium Times cewa mutane da dama sun sauya hanya inda suke tunanin an kawo hari ne fadar.

Mazaunin Kano ya ce sun ji harbe-harbe

"Matata ta kira ni kan cewa ana ta jin harbe-harbe a fadar Nasarawa, ana jin harbe-harben ne daga fadar."
"Mutane da suka nufi hanyar Ahmadu Bello suna sauya hanya, bamu san abin da ke faruwa ba har yanzu."

- Mazaunin yankin Nassarawa

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a tabbatar ba ko harbe-harben daga jami'an tsaro ne ko kuma fadawan sarki na 15 ba.

Kara karanta wannan

Masarautu: 'Karya ne' Gwamnati ta yi martani kan rahoton tashin hankali Kano

Kotun Kano ta ba da sabon umarni

A wani labarin, an ji wata babbar kotun jihar Kano ta dakatar da hambararrun sarakunan Kano biyar daga bayyana kansu a matsayin sarakai.

Haka zalika an ruwaito cewa kotun ta kuma umarci ‘yan sanda da su kori Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero daga gidan sarautar Nassarawa.

Wannan ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotun Tarayya ta bayar na dakatar da gwamnatin jihar daga rusa masarautu biyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel