Gwamnatin Kano Ta Nemi Alfarma Wajen Tinubu Kan Aminu Ado Bayero

Gwamnatin Kano Ta Nemi Alfarma Wajen Tinubu Kan Aminu Ado Bayero

  • Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf Kabir Yusif ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sa baki a rikicin sarautar Kano
  • Mataimakin gwamnan jihar wanda ya yi wannan kiran ya buƙaci Tinubu da ya fitar da Aminu Ado Bayero daga jihar
  • Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bayyana cewa tsohon Sarkin na Kano ya zama barazana ga tsaron jihar a halin yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga jihar.

Gwamnatin ta jaddada cewa kasancewar Aminu Ado Bayero a Kano yana barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: Gwamnatin Kano ta mika kokon bararta ga Shugaba Tinubu

Gwamnatin Kano ta bukaci Tinubu ya fitar da Aminu Ado Bayero daga Kano
Gwamnatin Kano ta bukaci taimakon Tinubu kan Aminu Ado Bayero Hoto: Abba Kabir Yusuf, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Kamfa_emirate_photography
Asali: Facebook

Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin a cewar jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: An zargi APC da jawo matsala

Aminu Abdulsalam ya gana da manema labaran ne dangane da rikicin sarautar da ke ci gaba da faruwa a Kano.

Jaridar The Punch ta ce mataimakin gwamnan ya zargi wasu mutane a cikin jam’iyyar APC da kitsa zanga-zangar nuna rashin amincewa da rusa masarautu da kuma dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano.

"A yau an gudanar da zanga-zangar da aka ɗauki nauyi wacce ƴan daban APC suka yi. Wasu mutane masu iƙirarin su masu ruwa da tsaki ne daga Bichi sun rubuto wasiƙa kuma dukkaninsu ƴaƴan jam'iyyar APC ne."
"Saboda haka yanzu abin gaba ɗaya an mayar da shi zuwa siyasa."

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: Bayan ya yi barazana, gwamnatin Kano ta ba Nuhu Ribadu hakuri

- Aminu Abdulsalam Gwarzo

Wace buƙata gwamnatin ta nema wajen Tinubu

Daga nan sai mataimakin gwamnan ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya sa baki kada al'amura su taɓarɓare.

Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ci gaba da cewa:

"Muna roƙon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su binciki abin da yake faruwa dangane da Aminu Ado Bayero."
"Sannan su ɗauki matakin gaggawa na fitar da shi daga inda yake zaune yanzu tare da fitar da shi daga cikin jihar nan. Saboda a yadda abubuwa suke a yanzu, yana zama barazanar tsaro a jiha."

Gwamnan Kano ya nemi afuwar Nuhu Ribadu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya nemi afuwa wajen mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Mataimakin gwamnan ya nemi afuwar ne bayan ya zargi Nuhu Ribadu da hannu wajen dawo da Aminu Ado Bayero zuwa cikin Kano bayan an tuɓe shi daga sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel