Gaskiya Ta Fito, Sarkin Dawaki Ya Faɗi Wanda Ya Tura Jirgi Ya Ɗauko Tsohon Sarkin Kano

Gaskiya Ta Fito, Sarkin Dawaki Ya Faɗi Wanda Ya Tura Jirgi Ya Ɗauko Tsohon Sarkin Kano

  • Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ya fayyace gaskiya kan yadda aka dawo da Aminu Ado Bayero cikin birnin Kano
  • Ɗanagundi ya ce babu ruwan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaron ƙasa, Malam Nuhu Ribadu a wannan lamarin
  • Wannan na zuwa ne bayan ofishin NSA ya yi barazanar shigar da ƙara kotu, amma daga baya gwamnatin Kano ta bayar da haƙuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Aminu Babba Ɗanagundi, Sarkin Dawaki babba a jihar Kano ya bayyana cewa shi ya shirya yadda aka dawo da tsohon sarki cikin birnin Kano.

Sarkin Dawakin ya tabbatar da cewa babu hannun Malam Nuhu Ribaɗu a dawo da tsohon sarkin gida kamar yadda mataimakin gwamna, Aminu Gwarzo ya yi zargi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Alhaji Aminu Ado Bayero.
Sarkin Dawaki ya ce shi ya kawo jirgin da aka ɗauko Aminu Ado aka dawo da shi Kano Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Babba Ɗanagundi ya faɗi haka ne a wata hira da kafar watsa labarai ta DW Hausa wanda ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Aminu Ado ya koma Kano

Yayin da aka tambaye shi game zargin da ake yi wa mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu, Ɗanagundi ya ce:

"Babu ruwan NSA a wannan lamarin, ni na samo jirgin da ya ɗauko Sarki Aminu Ado Bayero. Na ji mataimakin gwamna ya zargi Nuhu Ribaɗu, ina ga ya kamata ya nemi afuwarsa.
"Maganar sojoji kuma, dama kowa ya san aikin jami'an tsaro ne su tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, kuma har yanzun Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano.

- Aminu Babba Ɗanagundi

A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da ya nemo wa tsohon sarkin jirgin da zai hau ya yi tafiya kuma mutane da yawa da hakimai sun san haka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

Ɗanagundi ya ƙara da cewa ya yi tunanin Abba Kabir Yusuf zai yi biyayya ga umarnin kotu na dakatar da naɗa sabon sarki saboda ya amfana da hukuncin kotu.

"A matsayinsa na shugabanmu wanda ya amfana da kotu, tun da ita ta tabbatar masa da kujerar gwamna, na yi tsammanin zai bi umarnin da kotu ta bayar."

- Aminu Babba Ɗanagundi

Gwamnatin Kano da Nuhu Ribadu

Wannan na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan Kano ya yi zargin cewa NSA Nuhu Ribaɗu ne ya sa aka dawo da tsohon sarkin kano, Aminu Ado Bayero.

To sai dai bayan gaskiya ta bayyana, gwamnatin Kano ta fito ta bai wa Ribaɗu haƙuri kan kalaman Aminu Gwarzo.

Gwamnatin Abba ta roƙi Tinubu alfarma

A wani rahoton kuma, an ji Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya shiga tsakani kan rikicin da ke faruwa a masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Tsagin Ganduje ya mayar da martani kan abin da Gwamna Abba ya yi a Kano

Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, shi ne ya yi wannan kiran ga shugaban ƙasan domin hana jihar faɗawa cikin rikici.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262