'Yan Arewa Sun Fadi Abin da Gwamnatin Tinubu Take Bukata Bayan Shekara 1 a Mulki

'Yan Arewa Sun Fadi Abin da Gwamnatin Tinubu Take Bukata Bayan Shekara 1 a Mulki

  • Wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi jawabi kan cikar shugaban kasa shekara daya bisa mulki
  • Kungiyar ta bayyana irin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ta yi cikin shekara guda da kuma abin da ya kamata yan Najeriya su yi
  • Shugaban kungiyar, Dahiru Hammadikko ne ya yi jawabin a madadin dukkan yan kungiyar da ke yankin Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Wata kungiya mai goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi bayani kan cika shekara da shugaban kasar ya yi kan mulki.

Shugaba Tinubu
kungiya ta bukaci yan Najeriya su cigaba da marawa Bola Tinubu baya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tnubu.
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito shugaban kungiyar yana ba 'yan Najeriya hakuri kan halin da kasar ke ciki a yau.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya kai 'dan agajin Izala da ya dawo da kudin tsintuwa hajji

Har ila yau shugaban ya bayyana cewa suna fatan samun nasara a karshen al'amari saboda haka bai kamata yan Najeriya su cire tsammani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar shugaban kungiyar kan mulkin Tinubu

Shugaban kungiyar, Dahiru Hammadikko ya bayyana cewa yan Najeriya na bukatar hakuri da juriya domin kai kasar tudun na tsira, rahoton This Day.

Ya ce matuƙar ana bukatar samar da cigaba mai dorewa to dole sai an kara hakuri da juriya da kuma imani kan gobe za ta yi kyau. Ga abin da yake cewa:

"Matukar muna son cigaba to dole muyi imani da cewa gwamnati na kokari, dole muyi imani da cewa ana ƙoƙarin gyara mana gobe ne. Hakan zai bamu damar jure wahalar da muke ciki."
"Dukkan wahalhalun da muke ciki a yau suna nuna alama ne na cewar ana shirin kawo gyara domin tabbatar da gobe mai kyau ga Najeriya."

Kara karanta wannan

Tsohon jigon APC ya fadi yadda mulkin Tinubu ya fusata yan Najeriya cikin shekara 1

"Saboda haka bai kamata yan Najeriya su samu shakka kan cewa gobe za ta yi kyau ba. Ana bukatar mu cigaba da juriya da hakuri har mu cimma nasara."

- Dahiru Hammadikko

An soki Tinubu bayan cika shekara 1

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake fara shirye-shirye bikin cika shekara guda a mulkin Bola Tinubu, masana sun fara tofa albarkacin baki kan mulkinsa.

Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa cikin shekara daya, shugaban kasar bai tsinana komai ba sai kara jefa al'umma cikin wahalar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel