APC Za Ta Karbe Kudu Maso Gabas Idan Na Zama Gwamna, in Ji Chukwuma
- Mai neman takarar kujerar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar APC, Paul Chukwuma ya yi magana kan muradunsa na takara
- Paul Chukwuma ya ya sha alwashin cewa gaba daya jihohin Kudu maso Gabas za su dawo karkashin APC idan ya zama gwamna
- A cikin shirinsa na ganin nasarar APC, Chukwuma ya dauki hayar ofisoshin yakin zaben jam'iyyar a dukkanin mazabun jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Anambra - Tsohon mai binciken APC na kasa, Paul Chukwuma ya sha alwashin cewa gaba daya jihohin Kudu maso Gabas za su dawo karkashin jam’iyyar idan ya zama gwamnan Anambra.
Chukwuma ya fara kokarin takarar gwamna
Ya kuma yi alkawarin cewa nasarar da jam’iyyar za ta samu a zaben gwamnan jihar Anambra da ke tafe a 2025, zai zama wata babbar alama ta mamaye shiyyar a zabuka masu zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin shirinsa na ganin nasarar jam’iyyar, ya ce ya dauki haya tare da bayar da gudummawar ofisoshin yakin zaben APC a dukkanin mazabun jihar, in ji rahoton Leadership.
An ce Chukwuma ya mika makullan ofisoshin jam’iyyar ga mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na jiha karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Cif Basil Ejidike.
Chukwuma zai kara da Gwamna Soludo
Sir Paul Chukwuma, ya ce zai kayar da gwamnan jihar Anambra mai ci, Farfesa Charles Soludo idan ya lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a 2025.
Jaridar The Sun ta ruwaito dan siyasar yce zai rika shirya tarukan karawa juna sani a tsakanin shugabannin jam'iyyar a dukkan matakai na jihar.
Ya bayyana kudurinsa na baiwa jam’iyyar APC gagarumin goyon baya, tallafin kudi, da kwarin guiwa domin yin zarra a tsakanin jam’iyyun siyasa na jihar.
Gwamnatin tarayya ta yi karar gwamnoni
A wani labarin, mun ruwaito gwamnatin tarayya ta yi karar gwamnoni 36 na jihohin Najeriya a Kotun Koli domin nemawa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu.
Babban lauyan tarayya (AGF) kuma ministan shari’a ne ya shigar da karar karar mai lamba SC/CV/343/2024 a ranar 20 ga Mayu a madadin gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng