Basarake Ya Faɗi Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Mutum 50, An Yi Masu Jana'iza a Arewa

Basarake Ya Faɗi Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Mutum 50, An Yi Masu Jana'iza a Arewa

  • Rahotanni sun nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da ƴan bindiga suka kai yankin Wase ya karu zuwa 50
  • Basaraken Wase, Alhaji Ahmed Lawal, ya ce an yi wa mamatan jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a jihar Filato
  • Tun farko ƴan bindigar sun shiga kauyuka biyu a ƙaramar hukumar Wase, suka kashe bayin Allah 40 tare da ƙona gidaje da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai kauyukan Zurak da Bankalala a jihar Filato ya ƙaru zuwa 50.

Basaraken garin Wase a jihar Filato, Alhaji Ahmed Lawal ne ya bayyana haka inda aya ƙara da cewa tuni aka yi masu jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da jariri tare da mahaifiyarsa a jihar Kaduna

Gwamnan Filato, Celeb Mutfwang.
Basarake ya ce mutanen da suka mutu a harin ƴan bindiga sun ƙaru a jihar Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun farmaki ƙauyukan biyu da ke ƙaramar hukumar Wase, suka kashe mutum 40 a karon farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bayanai sun nuna adadin mutanen da suka mutu a harin sun ƙaru zuwa 50, ciki har da ƴan banga yayin da wasu mazauna da dama suka samu raunuka.

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Wase

Ƴan bindigar sun kuma ƙona gidaje da dama a harin, lamarin da ya jefa mazauna kauyukan cikin jimami da tashin hankali, rahoton Daily Trust.

A cewar mutanen yankin, lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na daren ranar Litinin a lokacin da mutane ke ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

An tattaro cewa mazauna garin ba su iya neman ɗauki daga jami'an tsaro ba saboda rashin sabis ɗin sadarwa a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a birnin tarayya Abuja, sun gamu da matsala

Wani shugaban matasan yankin, Sahpi’i Sambo, wanda ya tabbatar da kai harin, ya ce ‘yan bindigar sun shiga yankin ne a kan babura dauke da manyan makamai.

Ya ce daga zuwansu suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe gomman mutane, sannan suka raunata wasu da dama.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙaramar hukumar Wase, Daniel Manwan, ya ce jami'an tsaron DSS sun bi sawun ƴan bindigar kuma sun kashe uku daga ciki.

Ƴan bindiga sun shiga Abuja

A wani rahoton na daban, an ji 'yan bindiga sun sake kai hari yankin birnin tarayya Abuja, sun yi yunƙurin garkuwa da mutane 20 a daren ranar Lahadi.

Kwamishinan ƴan sanda na birnin Abuja da kansa ya jagoranci dakarun ƴan sanda suka kai ɗauki kuma suka yi nasarar dakile harin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel