Daraktoci da Manyan Ma'aikata Sama da 300 Sun Rasa Aikinsu a Babban Banki CBN
- CBN ya ƙara korar ma'aikata sama da 300 ciki har da daraktoci, mataimakan daraktoci, manyan manajoji da ƙananan ma'aikata
- Rahotanni sun nuna cewa daga ranar Alhamis zuwa Jumu'a, bankin ya raba gari da daraktoci 14 cikin 17 da suka rage waɗanda suka yi aiki da Emefiele
- Wannan kora ta sanya adadin waɗanda babban bankin ya sallama daga aiki ya kama hanyar 600 duk a wani yunkuri na gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) y ci gaba da tankaɗe da rairaya a cikin ma'aikatansa musamnan waɗanda suka yi aiki da Mista Godwin Emefiele.
A tsakanin ranar Alhamis zuwa Jumu'a, sama da ma'aikata 300 ne suka rasa ayyukansu a babban bankin CBN.
Wasu daga cikin ma'aikatan da aka kora ne suka tabbatar da haka ga jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa kusan dukkan daraktocin da suka yi aiki tare da tsohon gwamnan CBN an kore su, a yanzu jimullar ma'aikatan da aka kora a babban bankin sun doshi 600.
CBN ya kori daraktoci 14
A rahoton The Nation, aƙalla 14 daga cikin daraktoci 17 da suka yi aiki da tsohon gwamnan CBN Emefiele suna cikin waɗanda aka sallama a wannan karon.
Daraktocin da ke cikin rukunin waɗanda suka rasa aikinsu a makon jiya sun haɗa da Clement Oluranti Buari, Dokta Blaise Ijebor Lydia Ifeanyichukwu Alfa da Jimoh Musa Itopa.
Sauran sune Muhammad Abba, Rabiu Musa, Dakta Mahmud Hassan, Ozoemena S. Nnaji, Omolara Duke, Chibuike D. Nwaegerue, Chibuzo A. Efobi da Haruna Bala Mustafa.
Ragowar daraktocin da CBN ya sallama daga aiki sun kunshi, Rakiya Shuaibu Mohammed da kuma Benjamin Nnadi.
Jerin daraktocin da CBN ya bari
Sai kuma daraktoci uku da CBN ya ɗaga wa ƙafa a yanzu, Rashida Jumoke Monguno, darakta a sakatariyar kamfanoni, Salam-Alada Sirajuddin Kofo, darakta mai kula da harkokin shari’a da Aderinola Shonekan, daraktan bincike.
A wannan karon korar ma'aikatan ta shiga sassan CBN 29, kuma ta shafi ma'aikata tun daga daraktoci, mataimakan daraktoci, manajoji, manyan manajoji da ƙananan ma'aikata kamar masu ba da horo.
Bugu da ƙari, an tattaro cewa ma'aikatan da aka kora a yanzu suna aiki ne a rassan CBN da ke jihohi 36 da kuma hedkwatar babban bankin da ke Abuja.
CBN ya aike da saƙo ga ƴan canji
A wani rahoton kuma yayin da darajar Naira ke ƙaruwa a kasuwa, babban bankin ƙasa CBN ya yi wasu sababbin sauye-sauye domin inganta ayyukan ƴan canji.
CBN ya umarci halastattun ƴan canaji su sabunta lasisin aiki kuma ya cire masu dokar ajiye wasu adadin kudi kafin a ba su lasisi.
Asali: Legit.ng