Yadda Aka Yi Hasashen Dawowar Sanusi II Kuma Ta Tabbata Bayan Kwanaki 1538
- Muhammadu Sanusi II ya sake komawa gadon sarautar dabo, bayan an shafe kwanaki 1538 da cire masa rawani
- Hassan Sani Tukur yana cikin masu ba gwamna Abba Kabir Yusuf shawara, a 2023 ya yi hasashen rana irin Juma’a
- Kamar yadda Hassan ya yi magana a X a shekarar 2023, ranar Juma’ar da ya fada ne aka cikawa masoya burinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Yanzu maganar da ake yi, Muhammadu Sanusi II shi ne sarkin Kano, shekaru hudu kenan bayan an sauke shi daga kan mulki.
Dawowar Mai martaba kan karagar mulki bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gyara dokar masarautu ya jawo surutu iri-iri a yau.
Hassan ya ce Juma'a Sanusi II zai dawo
Legit Hausa ta ci karo da yadda daya daga cikin masu taimakawa gwamnan Kano, Abba Yusuf ya taba yin hasashen ranar nan a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Yunin 2023, Hassan Sani Tukur mai taimakawa gwamna a bangaren kafofin sadarwa na zamani ya nuna Khalifa zai dawo.
“A ranar Juma’a, da yardar Ubangiji da ikonSa, za a tabbatar da burin mutanen Kano.” - Hassan Sani Tukur
Sanusi II: Maganar da aka yi ta tabbata
Malam Hassan Sani Tukur ya yi hannunka mai sanda ne a lokacin, sakon nasa yana dauke da alamar rawani da ke nufin gidan sarauta.
Masu bibiyarsa a lokacin sun fahimci ana nufin za a maido Muhammadu Sanusi II mulki ko kuwa akalla a soke karin masarautun Kano.
Hasashen Adeniyi, Omojuwa kan Sanusi II
Olusegun Adeniyi wanda ya yi aiki a matsayin mai magana da yawun bakin Ummaru Yar’adua ya ce san za a ga rana irin ta yau.
A shafinsa na X, Mista Adeniyi ya dawo da wani tsohon rubutu da ya yi a This Day lokacin da gwamnatin Kano ta tsige Sarki a 2020.
Japeth Omojuwa wanda ya saba sharhi a kan abubuwan yau da kullum, ya yi farin ciki da jin cewa Sanusi II ya koma gadon sarauta.
A X, shi ma Omojuwa ya nuna dama can mai martaba zai sake zama sarki kuma a karshe sai gwamnati ta tsige sauran sarakuna.
Kwankwaso ya yi maganar Sanusi II
Ana da labari Rabiu Kwankwaso ya ce idan ya zo Kano, zai nemi bayanin yadda gwamnatin Abba Yusuf ta taba masarautu ba.
Rabiu Kwankwaso ya ce ba shi ya sa Abba ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II ba amma zai bincika domin fahimtar abin da ya faru.
Asali: Legit.ng