Kotu Ta Dakatar da Gwamnatin Kano Daga Mayar da Sanusi II Gidan Sarauta
- Babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar rushe majalisar masarautar Kano
- Mai shari’a Mohammed Liman ne ya yanke hukuncin a kan bukatar da wani basarake, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar
- Kotun ta umurci wadanda ake karar da su dakata da aiwatar da dokar rusa sarakunan har zuwa lokacin da za a kammala sauraron shari'ar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Watakila Muhammadu Sanusi II ba zai shiga gidan sarauta yanzu ba yayin da babbar kotun tarayya ta dakatar da gwamnatin Kano daga nada sabon sarki.
Kotun Mai shari’a Liman ta bayar da umurnin hana gwamnatin jihar Kano mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.
Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa alkalin ya bada umarnin ne a daren ranar Alhamis duk da cewa a halin yanzu yana kasar Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Dawaki Babba ya shigar da kara
Wani mai rike da sarautar gargajiya, Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba-Dan’Agundi ne ya shigar da kara gaban kotun ta dakatar da nadin sabon sarkin.
Wadanda ake kara a cikin shari’ar sun hada da: gwamnatin jihar Kano, majalisar dokoki, shugaban majalisa da babban lauyan gwamnatin Kano.
Sauran sun hada da: Kwamishinan ‘yan sanda, Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), jami’an tsaro na NSCDC da SSS ta jihar Kano.
Kotu ta dakatar da nada sabon sarki
Kotun ta bayar da umarnin a mika duk wasu takardu ko bayanan shari’a a kan IGP a Abuja, wanda ke wajen hurumin kotun, jaridar The Nation ta ruwaito.
Kotun ta umurci wadanda ake karar da su dakata da aiwatar da dokar rusa sarakunan har zuwa lokacin da za a kammala sauraron shari'ar.
Kotun za ta fara yin zama domin sauraron bangarorin da shari'ar ta shafa kan tauye hakki a ranar 3 ga watan Yuni, 2024.
Abba ya yi magana kan nada Sanusi II
Tun da fari, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya bayyana cewa maida tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi kan karaga, cika alkawari ne na yakin neman zabe.
A ranar Alhamis ne Gwamna Yusuf ya tsige Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano tare da mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng