Ganduje ya nemi a sa Sarkin Dawaki mai tuta da Chiroman Kano a majalisar masu nadin Sarki

Ganduje ya nemi a sa Sarkin Dawaki mai tuta da Chiroman Kano a majalisar masu nadin Sarki

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya mika bukatar gyara dokokin masarautar Kano na 2019 gaban majalisar jihar.

Kakakin majalisar jihar Kano, Abdul'aziz Gafasa, ya sanar da hakan ne a ranar Laraba da ta gabata a gaban majalisar.

Ana tsammanin 'yan majalisar zasu tattauna tare da yanke hukunci a kan bukatar kafin karshen watan Yulin 2020, jaridar Daiy Trust ta ruwaito.

Korarrun masu sarautar sun hada da Aminu Babba Dan Agundi wanda shine sarkin Dawaki Maituta da Sanusi Ado Bayero wanda shine Chiroman Kano.

Marigayi Ado Bayero ne ya kori Babban Dan-Agundi yayin da tubabben sarki Sanusi Lamido ya kori Sanusi Ado Bayero a kan zargin rashin biyayya.

Babba Dan Agundi ya kalubalanci tube masa rawani a kotu. Amma bayan shekaru 17 da aukuwar lamarin.

Kotun koli ta bai wa marigayi Ado Bayero gaskiya inda ta jaddada hukuncinsa.

Bayan da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya sake bukatar nada Babba Dan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, Ganduje ya bukaci majalisar da ta gyara wasu dokokin masarautar na 2019 wanda suka hada da dokokin masu nadin sarauta.

A halin yanzu, Sanusi Ado Bayero ne Wamban Kano kuma dan majalisar nada sarakuna idan majalisar jihar ta amince da bukatar.

Ganduje ya nemi a sa Sarkin Dawaki mai tuta da Chiroman Kano a majalisar masu nadin Sarki
Ganduje ya nemi a sa Sarkin Dawaki mai tuta da Chiroman Kano a majalisar masu nadin Sarki Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

A 2003, marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya kori Babban Dan-Agundi a matsayinsa na hakimin Gabasawa kuma Sarkin Dawaki Maituta bayan zarginsa da yayi da rashin biyayya tare da kutsawa cikin al'amuran siyasa.

Korarren basaraken, Babba Dan-Agundi ya ki halartar gayyatar da aka yi masa gaban kwamitin da marigayi Ado Bayero ya kafa don bincike a kansa.

Babba Dan-Agundi ya kalubalanci tube masa rawani da aka yi a babbar kotun jihar inda kotun ta bada umarnin mayar da shi.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa 'yan majalisar dattawa suka ki bari a san albashin da suke dauka - Wani Sanata ya fasa kwai

Masarautar Kano ta daukaka kara inda kotun ta sake bai wa Dan-Agundi gaskiya.

A karkashin sarautar Muhammadu Sanusi Lamido, masarautar ta sake daukaka kara inda kotun koli ta jaddada hukuncin masarautar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel